Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin, a jiya Litinin.
Zan iya cewa, wannan doka ta zo a dai-dai lokacin da ake matukar bukatarta, bisa la’akari da yadda wasu ’yan tsirarrun kasashe ke kakaba takunkumai bisa radin kansu domin cimma wani buri na kashin kai. Kana akasarin irin wadannan takunkumai kan haifar da illa maimakon gyara duba da cewa dama an yi su ne bisa son kai. Takunkumai irin wadanda bangare guda ke dauka, kan kawo tsaiko ga harkokin da suka shafi cinikayya da dangantaka tsakanin kasa da kasa, har ma da zaman lafiyar duniya da hadin gwiwar kasa da kasa.
- ECOWAS Za Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
- Ministan Lafiya Ya Yi Alƙawarin Inganta Tallafi Ga Likitoci A Hajjin 2025
Tarihi ya nuna cewa, ba a taba amfani da tukunkumai akai-akai kamar a yanzu ba, haka kuma yawan wadanda ake kakabawa takunkuman, ya fi yawa a yanzu. Tabbas kakaba takunkumi kan yi amfani idan aka yi bisa ka’ida da zurfin tunani da kyakkyawar niyyar gyara, kuma bisa rinjayen kasashe maimakon kasa daya tilo ko ’yan tsiraru.
Sai dai a yanzu kasashe musamman Amurka, kan kakaba takunkumai ne domin cimma wani buri da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe. Mun ga yadda ta rika kakaba takunkumai kan batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang da Hong Kong bisa fakewa da batun kare hakkin bil adama. Sai dai, takunkuman nata, illa suke neman haifarwa da dakile ci gaban kasar Sin da zaman lafiyar da al’ummar kasar ke mora.
Kowace ’yantacciyar kasa na da ikon tsarawa ko zabar manufofi da hanyoyin da suka dace da yanayinta da al’ummarta, kuma duk mun san cewa, moriyar al’umma shi ne gaba da komai cikin manufofi da ayyukan gwamnatin kasar Sin. Don haka, lokaci ya yi da ya kamata Sin ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, ta dauki matakan martani bisa dokokin kasa da kasa, domin jan kunne ga kasashen dake takalarta da neman ganin faduwarta. (Fa’iza Muhammad Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp