Wasu jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kori cafke babban editan fitacciyar jaridar Hausa ta Almizan, Malam Ibrahim Musa a Kano.
Musa wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da ibadar Umrah, lokacin da aka kama shi yana tare da rakiyar wata ‘yar uwarsa, Binta Sulaiman.
- DSS Ta Karyata Rahoton Kama Daya Daga Cikin Alkalan Kotun Zaben Gwamnan Kano
- DSS Ta Fara Cafke Wasu Kan Zargin Karkatar Da Tallafin Rage Radadi Na Jihohi
Jami’an tsaron sirrin na DSS sun dauke shi a filin jirgin saman Aminu Kano da safiyar Laraba.
Da yake magana a madadin ‘yan uwan editan na Almizan da ya shiga hannun, Abdullahi Usman, babu wani dalili da jami’an tsaron da suka ba iyalansa dangane da kamen.
Iyalan sun yi kira ga hukumar da ta saki Musa ba tare da gindaya wani sharadi ba cikin koshin lafiya.
“A halin da ake ciki, babu wani dalili da hukumomi suka bayar na kama shi duk da cewa ya shahara wajen kiran a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda aka kama shi a sakamakon kisan gilla da aka yi wa Mabiyansa 1000 da gwamnatin Nijeriya ta yi a shekarar 2015 a Zaria, jihar Kaduna.
“Kungiyoyin kare hakkin bil’adama, musamman kungiyar Amnesty International (AI), sun matsa wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufai, da ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatinsa ta binne mutane kusan 350 da aka kashe a yankin Mando jihar Kaduna.
“Muna kira da a gaggauta sakin Malam Ibrahim Musa a kuma ba shi kariya.” Cewar wani bangare na sanarwar.