Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Aisha Galadima, daya daga cikin magoya bayan siyasar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, a Kaduna.
Kamen Galadima, ya biyo bayan wani rubutu da ta yi ne a shafinta na Facebook, inda ta soki gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
- Za A Gyara Wuta A Inganta Lafiya Da Ilimi Da Kuɗin Tallafin Lantarkin Da Aka Janye – Ministan Labarai
- Yadda Aka Gudanar Da Hawan Daba A Ƙauran Namoda Da Naɗa Gwamna Dauda Sarauta
Idan dai ba a manta ba, a kwanakin baya ne Gwamna Sani ya bayyana irin dimbin basussukan da El-Rufai ya bar masa.
Jami’an tsaro na farin kaya ne suka dauke ta daga gidanta da ke Kaduna a ranar Lahadi da yamma.
Daya daga cikin ‘yan uwan Aisha Galadima ne ya tabbatar da kamem a wata tattaunawa ta wayar tarho da wata kafar yada labarai ta yanar gizo.
Kokarin tabbatar da kamen daga hukumar DSS ya cutura har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.