Jama’a barkanku da Sallah, barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira. Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda aka gudanar da shagulgulan sallah a gurare daban-daban, hadi da jin ta bakin matasa game da kalmar malan bahaushe da yake cewa ‘Ba a yin budurwa ranar Sallah’, tare da jin mahimmanci sada zumunci daga bakin matasa, musamman yadda kowa ya kai ziyara wajen ‘yan uwa da abokan arziki a wannan sallah. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka.
Sunana Siyama Abdul daga Jihar Kano:
An yi shagalin sallah sosai, wanda zai birge kowa, wanda daman an saba gudanar da shi a kowacce sallah, sai dai na kowacce sallah ya fi na kowacce. Eh! Toh da yawan mata su suke janyowa ake kallon ‘yan mata da wannan kalmar da zarar sallah ta zo, saboda suna fita kafin sallar a harbutse, ba sa kulawa da kansu sosai, wanda kamata yayi idan mace za ta fita ko da aike ne a ganta cikin shigarta tsaf, da tare da datti ba. Zumunci abu ne mai mahimmancin gaske, domin akwai lada me yawa cikinsa, yana da kyau al’umma su kasance masu sada zumunci ba lallaisai ranar sallah ba, yin zumunci yana kaho shakuwa da ‘Yan uwa. Ina gaida dukkanin al’ummar musulmi baki daya na kusa dana nesa, ina gaida iyayena da kannena, Allah ya maimaita mana Amin.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Yadda shagalin sallah ya kasance a unguwar mu yawancin mutane ba suyi azumi 30 ba, kowa ya fito lokaci daya an yi sallah kuma an gudanar da abun cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, abun gwanin ban sha’awa. Kalmar da ake cewa na ba a zabar budurwa ranar sallah, wanan kalma gaskiya ce saboda yawan cin ‘yan mata ba sa yin wanka sai lokacin wani shagalin ko sallah ko bukunkuna shiyasa ake cewa ba a yin buduruwa ranar sallah. Gaskiya ni ban yi buduruwa da sallar nan ba, batun zumunci yana da matukar muhinmanci da amfani zuwa ziyartar ‘yan uwa ranar sallah da zumunci ko a musulunci yana da amfani. Ina mika sakon gaisuwa ga ‘yan family dinmu Danguguwa Family gaba daya sanan kuma da abokai na.
Sunana Mudassir M2 daga Gwammaja Entertainment Jihar Kano:
Ana yin budurwa ranar sallah domin kana ganin nai tsafta ce daga baya kuma ashe kazama ce. Zumunci yanada amfani domin ana haduwa da ‘yan uwana wanda aka dade ba a hadu ba. Ina gaida musulman duniya ina yi wa kowa barka da Sallah.
Sunana Ibrahim Aminu Sarki daga Jihar Kano:
Alhamdulillah bikin sallah yayi kyau a garinmu Kano da unguwarmu Sharada. Wannan maganar haka take sakamakon me tsafta da mara tsafta ba a fiye ganewa ba. Abin a bayyane ya ke, zumunci abu ne me matukar kyau Allah da kansa ya ce da lokacinka zai riskeka a hanyarka ta zumunci da ka rabauta da Aljanna, Allah ya sa mu rabauta da Aljannar firdausi amin summa amin. Al’ummar musulmi baki daya ina yi musu barka da sallah, ina fatan an yi shagalolin Sallah lafiya na gode.
Sunana Musbahu Muhammad Daga Goron Dutse Kano:
An yi shagulgula lafiya da nishadi a cikin garin Kano da kewaye. Gaskiya ba a yin budurwa ranar Sallah, saboda wasu wankan sallar ne kawai. Ni ba zan iya yin budurwa a lokacin Sallah ba. Sada zmunci a lokacin sallah yana kara dankon zumunci da kaunar juna, sannan akwai nishadi sosai. Ina gaida dukkan ‘yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa, kuma ina fatan Allah ya maimaita mana.
Sunana Habiba Mustapha Abdullah daga Jihar Kano Karamar Hukumar Nassarawa:
An yi bikin sallah lafiya jama’a kowa yana cikin farin ciki an ci an koshi an yi hanikan, wannan magana ce ta malan bahaushe ba a saurayi ranar sallah ni dai ban yi ba. A gaskiya sada zumucin yana da amfani sosai ga tarin lada. Ina gaida Yaya Abba Saiyada da Ango, Anti Aisha M&E wadda take aiki a Asibitin Gama Model PHC, Allah ya nuna mana wasu shekarun cikin lafiya da kwanciyar hankali Allah ya maida kowa gida lafiya.
Sunana Abbale Ismail daga Jihar Kano:
Gdiya ta kara tabbata ga fiyayan halita Annabinmu (s a w). Gaskiya bukukuwan sallah ya kayatar dani sosai ganin yadda maza da mata suke walwala da nuna jin dadi, kuma nayi farin ciki wanda ba zai musaltu ba. Hmmm gaskiya game da wadanda suke cewa ba a budurwa ranar sallah sai na ga kamar zolaya ce kamar yadda hausawa suke cewa mai kyau ba ta kwantai, to a cikin dubu indai ka duba to za ka samu indai mai kyau din ka zaba. To da farko dai ina mika gaisuwata ga kungiyar mu ta Guntun Gatarinka Ya fi sari Ka bani, ina mika gaisuwata ga Ya’u dan zariya, ina mika gaisuwata ga ‘yan uwana Wasila, Shamsiya, Ummi da Surajo, Munzili da Ashiru da Aliyu naira yayi onazee soja da sauransu fatan kun yi sallah lafiya.
Sunana Hannatu Musa Dogarai daga Gwammaja Entertainment Jihar Kano:
An yi shagalin bikin Sallah lafiya, Masoya da ‘yan uwana da abokan arziki ina yi wa kowa fatan alkhairi, ubangiji Allah ya karbi ibadun mu, Allah ya sa muna daga cikin ‘yantattun bayi ameen. Sakon barka da sallah tare da godiya ga jigona tsanina wato mai girma babana Yakubu Furodusa Gwammaja, tare da Yayana Jagoran Mayafin Sharri, ubangiji Allah ya ci gaba da dafa mana, Allah ya daukaka kamfanin gwammaja ya kuma hada kanmu na samu nasarori da yawa sosai, wanda cikin ikon Allah nayi fims ta karkashin wannan company. Inda har na samu nasarar lashe role din Talatu Busy. masha Allah barkanmu da sallah.
Sunana Dr. Mohammed Ismail
Alhamdulillah mun yi shagulgulan sallah lafiya kalau a garin mu, sannan kuma gaskiya abinbda ‘yan uwanmu musulmai na shagulgulan sallah a Maiduguri abu ne da ya burge ni kuma na ji dadi. Yin budurwa ranar sallah ra’a yi ne, amma ko ni din nan ba zan yi budurwa ba ranar sallah, saboda ba za ka iya gane asalin kyaun ita budurwar ba, saboda duk wacce ka gani kyakkyawa ce kuma koma abin ya bawa a wannan lokacin. Zumunci babban abu ne wanda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya umurci da mu zama masu tsada zumunta ga ‘yan uwan mu musulmai. To anan idan ka tsaya ka duba sada zumunta ranar abu ne da yake da matukar kyau, Ina me mika sakon gaisuwa ga ilahirin Musulmai duniya baki daya, ina fatan Allah ya sa ibadun da muka yi a watan Ramadana karbabbu ne, Allah ya nuna mana wani shekarar rai da lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp