Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta cafke wata budurwa da ta kware wajen satar wayar matan Aure bayan sun bata aminci a jihar.
Budurwar mai suna Shamsiyya Adamu ‘yar shekara 19, ta shiga hannu ne tare da abokan aikinta su biyar, an gano ta ne biyo bayan korafe-korafen jama’a da aka shafe watanni ana yi kan yawaitar satar wayar salula a cikin birnin Kano.
- Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
- Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Yarinya Ɗaya da Mutum 2 A Kaduna
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, Shamsiyya, wacce ke zaune a Birget kwatas a Kano, ta dauki hayar dan Adaidai da wanda ya kware wajen fasa asusun banki ta wayar salula, in ta afka gidan matan Aure sai ta yaudare su ta sace wayar, dan Adaidaita kuma yana jira a waje, sai ya kai ta wurin mai fasa asusun banki, ya kwashe kudaden wacce aka sace ma wayar.
Kamen da aka yi mata a ranar 21 ga watan Disamba, 2024, ya kawo karshen binciken da wata runduna ta musamman da kwamishinan ‘yansanda, CP Salman Dogo Garba ya kaddamar kuma ya jagoranta.
Wadanda aka kama dake aiki da ita akwai Idris Yusuf, dan shekara 23, mai sana’ar Adaidaita da ke tuka Shamsiyya zuwa wuraren da take aikata laifuka; Al’asan Dahiru, mai shekaru 24, wanda ya kware wajen boye kayayyakin da aka sace; Abdulmajid Haruna, mai shekaru 27, mai siyan kayan sata, wanda aka kwato wayoyi shida daga hannunsa, da Salim Auwalu, mai shekaru 21, wanda ya kware wajen fitar da kudi daga asusun ajiyar banki.
Rundunar ‘yansandan ta bayyana cewa an shigar da kararraki 30 a kan Shamsiyya kan satar waya ta hanyar yaudara, 29 daga cikinsu mata ne.