Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, duk da kokarin da ta ke yi da kuma yin aiki da masu hadaka don yakar cutar cizon Sauro a kasar ana samun kashi 27 na mutuwar wadanda suka kamu da cutar, inda kuma mutanen da ke mutuwa a duniya suka kai kashi 32.
An kuma kiyasta cewa, ana da yawan cutar da ta kai miliyan 55, inda kuma ake da kusa da sauran cututtukan da suka kai yawan 90,000 da ke aukuwa a duk shekara.
Ministan kiwon lafiya na kasar nan Dakta Osagie Ehanire a jawabinsa a lokacin tunawa Sa zagoyowar ranar yaki da cutar ta shekarar 2003 ya koka kan yadda cutar ke shafar tattalin arzikin kasar nan bayyana cewa,
Osagie ya ci gaba da cewa, wanda ya harbu da cutar ba ya iya zuwa makaranta, ofis ko kuma kasuwa, inda hakan ke yiwa tattalin arzikin kasar nan nakasu da kuma rage samun kudin shiga a gare su.
Ministan wanda Mamman Mahmuda, babban sakatare a ma’aikatar ya wakilce shi a wajen taron bayyana cewa, abinda ake kashewa a fannin na cutar, an kiyasta ya kai sama da kashi 70, inda ‘yan Nijeriya ke kashe Naira 2,280.00.
Ya ce, nauyin tattalin arzikin da ake kashewa a Nijeriya ya kai dala biliyan 1.6 wanda ya yi dai dai da Naira biliyan 687 a shekarar 2022, inda hakan zai iya karuwa zuwa kimanin dala biliyan 2.8 wanda ya yi dai dai da Naira tiriliyan 2 a shekarar 2030.
Ya ce, yana da kyau a dakile yaduwar cutar, musamman don a rage talauci kara bunkasa fannin kiwon lafiya, don a cimma burin da ke da shi na cimma muradun karni, inda ya ce, dole mu ci gaba yakar cutar don a cimma burin da ake da shi na kakkabe ta kafin zuwan shekarar 2030, dai dai da burin da kungiyar kiwon lafiya ke WHO ke son cimma.