Kungiyar kwararrun likitocin larurorin mata da kananan yara ta Nijeriya (SOGON) ta bayyana cewa duk likitan mata a Nijeriya na kula da mata 6,000 maimakon 400.
Mataimakin shugaban jami‘ar koyar da kimiyyar lafiya ta gwamnatin tarayya, da ke garin Azare a Jihar Bauchi, Farfesa Bala Muhd Abdu, kuma daya daga cikin manyan jami’an Kungiyar SOGON, ya bayyana hakan a lokacin taron kungiyar SOGON karo 57 da ya gudana na kwana hudu da ya gudana a Jihar Kano.
- Kamfanonin Siminti Ke Haifar Da Kashi 7 Na Dumamar Yanayi A Duniya – Dangote
- Gwamna Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Binciken Matsalolin Aiki Hajji
A takardar bayan taro da ya karanta ga manema labarai, shugaban kungiyar SOGON na kasa, Dakta Habib Sadauki, ya ce karancin likitoci da kayan aiki shi ne ke haddasa yawan mutuwar mata da jarirai a Nijeriya.
Ya ce Nijeriya ce ta biyu a kasashen duniya wajan yawan mutuwar mata a lokutan haihuwa da rainon ciki wanda ake bukakatar gwamnatin tarayya da na jihohi su ware makudan kudadede a kasafin kudin wajen inganta wannan fani.