A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Adadin ribar da aka samu a manyan kantuna da gidajen abinci a cikin kwanaki hudu na farkon hutun ta karu da kashi 3.3% idan aka kwatanta da na bara, kuma har zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan, kudin shiga da aka samu daga kallon fina-finai yayin wannan biki ya wuce RMB Yuan biliyan 1.8 kwatankwacin fiye da dala miliyan 252.
Duniya ta ga ci gaban Sin na dogon lokaci. A daidai wannan lokacin hutu, wasu tsirarun kasashe sun fara daukar sabbin matakan buga haraji, yayin da kasar Sin ke shirya sabbin damarmaki na bude kasuwarta ga duk duniya. Bugu da kari, a watan Oktoba da muke ciki, za a gudanar da cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a birnin Beijing, inda za a tsara shirye-shirye da dabarun ci gaban kasar na shekaru biyar masu zuwa, sannan a watan Nuwamba mai zuwa, za a sake bude baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare zuwa nan kasar Sin karo na 8, inda kasashe da kungiyoyin duniya da dama suka tabbatar da halartar baje kolin, kuma kamfanoni sama da 3,200 daga kasashe da yankuna sama da 110 sun tabbatar da halarta. Kamar yadda kamfanoni na duniya da yawa suka bayyana cewa, kasuwar kasar Sin ta bambanta da ta sauran kasashe, wanda ke nuna damarmakin kasuwanci masu yawa da ba za a iya kubuce ba. (Amina Xu)