Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a kasashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a Najeriya ya rawaito.
Kwamishinan Ecowas Abdel-Fatau Musah ya fadi hakan ne a Abuja cewa kungiyar na bukatar tara Dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda kasashe mambobin kungiyar suka bayar da rabin adadin.
“A yau, Burkina Faso ta zarce Afganistan a matsayin kasa mafi fama da ta’addanci a duniya kuma Afirka ta zama gida ga kungiyoyin ta’addanci,” in ji Musah.
Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso da Nijar dai sun janye daga kungiyar ta Ecowas a farkon wannan shekarar, bayan da suka zarge ta da rashin tallafa musu wajen tunkarar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin al-Kaeda da IS a tsawon shekaru.