Jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) na shiyyar Gombe, sun kama wasu mutane 21 da ake zargi da damfarar Intanet a Jihar Bauchi.
A cewar wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin, “An kama wadanda ake zargin ne ta hanyar samun sahihan bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na damfarar Intanet a yankin Kaure New Government Reservation Area, Bauchi da Awala, a titin Maiduguri, Jihar Bauchi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Rukunin Farko Na Taraktoci Dubu Biyu Daga Belarus
- Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi
“Abubuwan da aka kwato daga hannunsu a wajen kama su sun hada da motoci kirar BMW daya da Toyota Camry, PlayStation 5 guda uku, wayoyi masu tsada 30, da babbar talabijin daya, injin PoS guda shida, iPad guda hudu, da kwamfyutoci biyar.”
Sanarwar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp