A ranar Talata 25 ga Fabrairu, 2025, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa, EFCC reshen jihar Legas, ta gurfanar da wasu ‘yan kasar Sin 16 a gaban mai shari’a Daniel Osiagor na babbar kotun tarayya da ke zaune a Ikoyi, Legas bisa laifin zamba.
Ga sunansu kamar haka: Hu Hui (A Bin), Liao Ri Xing (Li Jun), Li Qiang (Yang Huan Huan), A Wen, Da Tou, Cheng Jian, Cong Bing, Fei Fan, Huxi Heng, Zheng Wei (Hong), Huang Leng, Huang Zhi, Huang Zhi, Zha Whi, Sun Hao, da Lu Qiang.
- Darajar Naira Ta Farfaɗo A Kasuwar Hada-Hadar Kuɗi Ta Duniya
- Ministan Gidaje, Ba Ɗan Jam’iyyar APC Ba Ne – Shugaban APC Na Kano
Suna daga cikin mutane 792 da ake zargin jami’an EFCC sun kama a Legas, a wani samame da aka yi wa lakabi da “Eagle Flush Operation”.
An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri.
Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai lauyan masu shigar da kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’ar tare da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali.
Mai shari’a Osiagor ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a, sannan ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp