Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta mika takardun kadarorin gidaje 324 na ‘yan fansho na jihar Kano da aka kwato ga ‘yan fansho na jihar.
A cewar hukumar EFCC, an sayar da gidajen ne bisa damfara ga wasu abokan tsaffin gwamnonin jihar Kano biyu da aka sakaya sunayensu.
- EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfara 4 A Borno
- Kashi 70 Na Badakalar Kudade A Nijeriya Na Da Alaka Da Bankuna – EFCC
Yayin da yake mika takardun kadarorin guda 324 da kudinsu ya kai Naira biliyan 4.1 ga ‘yan fansho a ranar Litinin, kwamandan hukumar ta EFCC na shiyyar Abuja, Mataimakin Kwamandan EFCC, Adeniyi Adebayo, ya tabbatar da cewa, EFCC za ta ci gaba da yin iyakacin kokarinta na ganin ta dakile yawaitar ayyukan zamba da ha’inci acikin al’umma.
Wakilan hukumar fansho ta jihar Kano, Alhaji Hassan Muhammed Aminu, Kubra Ahmad Bichi da Salisu Yakubu Abubakar, wadanda suka karbi takardun a madadin ma’aikata da ‘yan fansho, sun bayyana jin dadinsu da hukumar EFCC ta taimaka musu wajen kwato gidajen.