Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) Ola Olukoyede, ya mika katafaren jerin gidaje 750 na alfarma da aka kwace daga hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ga Ministan Gidaje, Ahmed Musa Dangiwa.
An mika takardun ne bayan wani takaitaccen taro da aka yi a Abuja, ranar Talata.

Ministan ya ce, za a sayar da gidajen ne ta hanyar bayyanannen tsari da ya dace.
“Za a yi amfani da ingantaccen tsari wajen sayar da gidajen ta hanyar shafin intanet na sabunta fata, da gwamnatin Tinubu ta kirkiro,” in ji shi.
