Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bar ofishin EFCC da ke Abuja sa’o’i bayan da ya mika kansa ga hukumar a ranar Laraba domin amsa gayyatar da ta yi masa kan badakalar kudade har naira biliyan 80.2
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, hakan ya biyo bayan ‘yar ɓuya da aka kwashe watanni ana yi tsakanin jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma tsohon gwamnan.
- Yahaya Bello Ya Amsa Gayyatar EFCC
- Firaministan Sin Ya Taya Murnar Bude Taron Hukumar IAEA Karo Na 68
Idan dai ba a manta ba, EFCC ta bayyana neman Bello ruwa a jallo bayan ya kasa amsa gayyatar da hukumar ta yi masa, sannan kuma bai bayyana a gaban kotu ba domin amsa tambayoyi bisa tuhumar sa da aikata laifin ɓarnatar da dukiyar al’umma.
Sai dai a ranar Laraba, Bello tare da rakiyar, Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, sun isa hedikwatar EFCC, a cewarsa, domin girmama gayyatar da hukumar ta yi masa, tare da wanke sunansa daga zargin.
Amma, bayan haka, tsohon Gwamna Bello, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ofishin yada labarai na Yahaya Bello, Ohiare Michael, ya ce, Bello ya bar hedikwatar EFCC ba tare da an yi masa tambayoyi ba bayan jami’anta sun nemi ya wuce.
EFCC ba ta mayar da martani ga LEADERSHIP ba kan ikirarin Bello ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.