Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ce ta kammala shirye-shiryen kama wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke karewa wadanda ake zargi da ayyukan rashawa, da kuma wasu gurbatattun masu rike da mukaman gwamnati bayan miÆ™a mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
BBC ta ce, shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, shi ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da Jaridar Daily Trust.
- EFCC Ta Cafke Wasu Mutane 20 Da Take Zargi Da Sayen Kuri’u A Kwara
- EFCC Ta Gurfanar Da Farfesa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N1.4bn
Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan waÉ—anda suke shirin kamawa ba da zarar sun suka daga kan mulki.
A Nijeriya dai, gwamnoni na cikin jami’an gwamnati da ke da kariya wadda ya hana a a kama su idan suna kan mulki.
Shugaban na EFCC ya ce akwai ma’aikatun gwmanati guda biyu da hukumar ke bincike a kansu a halin yanzu saboda ayyuka da suka saÉ“a wa ka’ida da suke yi.
A cewarsa, a ɗaya daga cikin ma’aikatun an yi almundahanar kuɗaɗe ta N4bn na wasu kwangiloli kusan 20 da.
Bawa ya ce, “A yanzu haka, muna binciken ma’aikatu biyu da aka biya kuɗaɗen har sau biyu a cikinsu.
“Waɗannan kwangiloli ne da aka yi tun shekarar 2018, sannan wasu mutane masu karfin hali suka fito da suka bayyana batun.
Ya ce an buga takardun bogi a cikin ma’aikatun, sannan da haÉ—in-bakin wasu ma’aikata, aka kirkiri takardun karya tare da biyan kuÉ—i.
Bawa ya ce muddin aka mayar da harkoin gwamnati ta hanyar zamani, ba za a samu irin waɗannan badaƙaloli ba.