Tsohon shugaban marasa rinjaye kuma tsohon Sanata mai wakiltar kudancin Jihar Taraba, Sanata Emmanuel Bwacha, ya sake lashe zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar.
Bwacha, ya yi nasaran kada mutum biyar da suka shiga zaben fidda gwanin da kuri’u 778, cikin 791, da aka kada.
- Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Gina Budadden Tsarin Raya Tattalin Arzikin Duniya
- Wani Ya Rasu Yayin Da Magoya Bayan APC Da PDP Suka Yi Arangama Da Juna A Jigawa
Shugaban kwamitin gudanar da zaben kuma tsohon shugaban rundunar sojin kasa, Laftanar Tukur Buratai (mai ritaya), ya sanar da haka bayan kammala zaben.
Ya ce Sanata mai wakiltar Taraba ta Tsakiya, Sanata Yusuf Yusuf, ya zo na biyu da kuri’u biyar, ya ce David Kente, Danladi Kifasi, Saleh Mamman da Anthony Manzo, ba su samu ko kuri’a guda ba.
Da yake magana da manema labarai bayan sanar da sakamakon zaben Emmanuel Bwacha, ya ce “Duk da jam’iyyar APC jam’iyyar adawa ce a Taraba, amma yanzu lokacinta ne, zan tabbatar na lashe zaben gwamna.
“Ina mai bai wa mambobin jam’iyyar APC a Taraba zan tafi da kowa, ina kira ga abokan takara ta da su dauka haka Allah ya nufa, mu hadu mu yi aiki tare domin nasarar jam’iyyarmu a Taraba,” in ji Bwacha.