Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF), ta naɗa tsohon kocin Mali, Éric Sékou Chelle, a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles.
Chelle, mai shekara 47, ya taba jagorantar Mali har zuwa zagayen kwata-fayinal a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 kafin su sha kaye a hannun mai masaukin baki, Ivory Coast.
- Awannin Da Sallamarsu A Matsayin Kwamishinoni, Gwamnan Bauchi Ya Naɗa 3 A Matsayin Mashawarta
- Ana Kara Zuba Jarin Waje A Kasar Sin A Sabuwar Shekara
A wata sanarwa da NFF ta fitar, ta ce Chelle zai fara aiki nan take tare da mayar da hankali kan nasarar Nijeriya a wasannin neman gurbin Kofin Duniya na 2026.
Sai dai hukumar ba ta bayyana tsawon kwantaragin da ta yi da shi ba.
Naɗin Chelle ya biyo bayan gazawar NFF wajen cimma matsaya da ɗan ƙasar Jamus, Bruno Labbadia, kan batun haraji bayan an sanar da ba shi aikin a watan Agustan 2024.
Chelle, wanda ya taka leda wa Mali sau huɗu, zai kuma jagoranci tawagar ‘yan wasan cikin gida na Super Eagles a gasar CHAN, inda wasannin neman gurbi ke gudana a yanzu.