Rahotanni da bincike sun tabbatar da cewa, Manhajar Facebook ta goge asusun Mawakin Siyasa, Dauda Adamu Rarara mai mabiya fiye da miliyan 1, a ranar Asabar.
Yayin da muka binciki asusun a lokacin rubuta wannan rahoton a ranar Lahadi, asusun babu shi.
- Jami’an DSS Sun Cafke Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara
- Mahaifiyar Rarara Ta Kubuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga
An ce, ‘yan Nijeriya ne suka kai rahoton asusun bayan da ya dora wakar yabon Shugaba Bola Tinubu a asusun duk da tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke ciki na hauhawar farashin kayayyakin abinci.
“Tinubu ya Inganta Nijeriya. ‘Yan Arewa sun yi bankwana da yunwa da rashin tsaro da fatara,” in ji Rarara a cikin wakar.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar, dangane da tabarbarewar tattalin arziki a Nijeriya.
In ba a manta ba, kwanan nan ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara, Hajiya Hauwa’u Adamu a kauyen Kahutu, da ke karamar hukumar Danja ta jihar Katsina.
An sako Hajiya Hauwa’u ne bayan ta shafe kwanaki 20 a hannu ‘yan bindigar, kamar yadda wata majiya ta kusa da danginta ta bayyana.