Fadar shugaban ƙasa ta sanar da sallamar Fegho John Umunubo, wanda mai taimaka wa mataimakin shugaban ƙasa ne, a ɓangaren bunƙasa tattalin arziki na zamani.
Hakan ne ƙunshe ne, a cikin sanarwar da daraktan yaɗa labarai da huɗɗa da jama’a na fadar shugaban ƙasa Abiodun Oladunjoye, ya fitar.
Sanawar ta bayyana cewa, dakatarwar da aka yiwa Umunubo, ta fara aiki ne, nan take.
- Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata
- Ganawata Da Macron Ta Yi Amfani – Tinubu
“Masu ruwa da tsaki da ke a fannin da ke a cikin ƙasar nan da kuma waɗanda suke a ƙetare, su kasance a ankare da wannan sanarwar ta dakatarwar ta Fegho John Umunubo, har da kuma ɗaukacin alummar ƙasar kan,”. A cewar sanawar.
Kazalika, sanarwar ta kuma gargaɗi Umunubo kan gabatar da kansa ko kuma wakiltar mataimakin shugaban ƙasar a dukkanin wato taro, inda kuma ta gargaɗi kan yin duk wata huɗɗa da shi, da sunan ofishin na mataimakin shugaban ƙasa.
A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo.
Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Idan za a iya tunawa, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa, ba ta fitar da wata ƙwaƙwarar sanarwa, kan maƙasudin soke takardar ɗaukar aikin da aka yiwa Umunubo ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp