Kimanin watanni 10 ke nan da za a fara aiwatar da tsare-tsaren da za su kai ga zabuka masu zuwa a fadin kasar nan, masana harkokin siyasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar adawa ta PDP, suna ta fadi tashin ganin wa zai iya kokawa da kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Bayan shan kaye a jere a zabukan shugaban kasa har guda uku, PDP na neman sabuwar hanyar da za ta taka ta kai ta ga nasara a 2027.
- Kasar Sin: Ba Makamai Da Takunkumai Ake Bukata Wajen Warware Rikicin Palasdinu Da Isra’ila Ba
- Babban Masallacin Adogba: Sultan Da Makinde Sun Kafa Turbar Kawar Da Bambancin Kabilanci Da Na Addini A Nijeriya
Wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, kamar yadda wani masanin tarihin kasar Amurka, Allan Lichtman, wanda ya yi suna wajen yin hasashe guda tara daga cikin 10 na zaben shugaban kasa na baya-bayan nan da aka yi a kasar Amurka, sun ce sun yi na’am da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin wanda zai iya lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar a 2027.
Duk da cewa yunkurin Makinde na neman shugabancin kasar ya ci gaba da zama hasashe ne, amma alamu na nuni da cewa ba wasu tsiraru ne a jam’iyyar ba ne suka amince da karfin tikitin Makinde.
A yayin da al’ummar kasar ke cikin mawuyacin hali, sakamakon tabarbarewar farashin man fetur, karin kudin wutar lantarki, da faduwar darajar Naira, ‘yan Nijeriya na sake fahimtar kaifin sakamakon zaben 2023, wanda ya sanya jam’iyyar APC ta ci gaba da kasancewar a kan mulki.
A don haka, kwadayin samun canjin shugabanci a matakin kasa ya haifar da kwarin gwiwa wajen ganin an gina tubalin da zai kai mu zuwa shekarar 2027, wanda aikin da ake yi na samar da tsarin siyasa ba zai wadatar kadai ba idan ba a gabatar da wani babban dan takara ba mai nagarta ba.
Duk da rigingimun cikin gida da ke cikin jam’iyyar PDP, wasu masu ruwa da tsaki sun hakikance a kan cewa hanyar da jam’iyyar za ta bi wajen samun nasara a zaben 2027 shi ne ta tsayar da dan kasuwan nan kuma dan asalin Jihar Oyo wanda ya kasance dan siyasa ne a matsayin dan takararta wanda shi ne zai kayar da zabin APC na kai tsaye na Shugaba Bola Tinubu.
Ga manyan masu ruwa da tsaki da suke da wannan ra’ayi, sun ce Gwamna Makinde yana da kwarjini da kuma tsarin da zai kai PDP ga samun nasara a 2027.
Ba kamar yadda jam’iyyar PDP ta zabi dan takarar Arewa a zaben shugaban kasa na 2023 ba, masana da masu ruwa da tsaki na ganin cewa ya kamata dan takarar kudancin kasar ya daga tutar jam’iyyar a 2027.
A cewarsu, wannan matakin zai warkar da raunukan da ‘yan kudancin kasarnan suka samu sakamakon fitar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023.
Bisa haka ne, a kwanakin baya wasu masu ruwa da tsaki suka fara yakin neman ganin Makinde ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
Kungiyar da ke karkashin inuwar ‘Progressibe Youth for Makinde Presidency 2027’ a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ta bayyana cewa, Makinde ya nuna nagartattun halaye na shugabanci da jajircewa wajen gudanar da shugabanci na gari, wanda hakan ya sa ya dace da shugabancin Nijeriya.
Kungiyar ta fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na Makinde ne a watan Yunin wannan shekara. Duk da cewa yakin neman zaben na Makinde 2027 ya takaita ne a shafukan sada zumunta, sakon na su ya yi daidai da kyakkyawan jagoranci na Gwamnan Jihar Oyo.
Wani fitaccen mai goyon bayan Makinde, Olamilekan Kehinde, wanda bai boye yunkurinsa na ganin gwamnan ya tsaya takara a zaben shugaban kasa a 2027 ba, ya bayyana kwarin guiwarsa kan Makinde, inda ya ce Makinde ya nuna nagartattun halaye na shugabanci da jajircewa wajen gudanar da shugabanci nagari, wanda hakan ya sa ya dace da shugabancin Nijeriya idan aka kwatanta da shugabancin kasar a yanzu.
Da yake tabbatar da hakan, kungiyar ‘Oyo Renaissance Group’, ta bayyana Makinde a matsayin mutum mai jajircewa a jam’iyyar wanda bai taba watsi da manufa da muradin jam’iyyar PDP ba.
Kodinetan kungiyar Kwamared Dayo Adedoyin, a wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, ya ce, “Gwamna Makinde ya nuna halayensa na jagoranci da kuma kwazonsa wajen cika alkawuran da ya yi wa al’ummarsa a jihar Oyo a cikin jerin ayyuka da manufofin da ya dace ga al’umma wanda ya dauki lokaci yana gudanarwa a matsayinsa na gwamnan Jihar Oyo daga 2019 zuwa yau.
“Gwamna Makinde ya tsayu kyam wajen tafiyar da jam’iyyar kuma zai ci gaba dayin aiki tare da takwarorinsa gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP a jihohi daban-daban na tarayya ta hanyar aiwatar da manufofi da tsarin jam’iyyar.”
Bincike ya nuna cewa Makinde bai taba gujewa zama dan cikakken dan jam’iyya ba. Har wala yau bincike ya nuna cewa gwamnan tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019, ya ci gaba da tallafa wa ma’aikatan PDP a Sakatariyyar jam’iyyar na kasa, da kuma Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar (NWC) da Hukumar Amintattu (BoT).
Shi kadai ne ya ba da kudi wajen gina sabon ofishin Cibiyar Dimokuradiyyar Al’umma mai suna ‘Peoples Democratic Institute (PDI)’, wanda cibiya ce ta zurfafa tunani na jam’iyyar, aikin da ya lakume daruruwan miliyoyin naira.
Domin ci gaba da nuna jajircewarsa na ci gaban jam’iyyar ba tare da wata tangarda ba, Makinde ya gina Sakatariyar jam’iyyar PDP shiyyar Kudu maso Yamma a Ibadan tare da sanya mata sunan shugaban jam’iyyar, Hon. Soji Adagunodo wanda ya rasu yana kan mulki. Za a kaddamar da ginin nan ba da jimawa ba.
A baya-bayan nan ne ya biya dukkan ma’aikatan sakatariyar jam’iyyar PDP na kasa alawus-alawus din gidaje da suka hada da masu taimaka wa jam’iyyar na NWC da kudi kusan Naira miliyan 300.
Da yake tantance yiwuwar nasarar jam’iyyar PDP a 2027, manazarci kan al’amuran al’umma kuma shugaban kungiyar ‘Reset Lagos PDP’, Dakta Adetokunbo Pearse, ya tabbatar da cewa, PDP na da kyakkyawar damar darewa kan kujerar shugabancin kasa a 2027 duk da rikicin cikin gida da yake cikin jam’iyyar. Ya kuma yi imanin cewa damar jam’iyyar zai kai gaci ne idan aka bai wa Makinde dama a matsayin dan takara.
“Masu sharhin siyasa da ke tunanin cewa akwai matsalar shugabanci a PDP sun yi kuskure sosai. Mukaman shugabanci a dukkan matakai na jam’iyyar yana nan a yadda yake. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar dadadde, Sanata Wabara shi ne shugaban kwamitin amintattu (BoT), Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, kuma Ambasada Umar Iliya Damagum shi ne shugaban riko na kasa na jam’iyyar,” in ji Pearse.
Pearse, wanda tsohon memba ne na Majalisar Kamfen din Shugaban Kasa na PDP a 2023, ya ci gaba da cewa, sabanin ra’ayin da ake yadawa al’umma, PDP ba ta tsayar da tikitin takarar shugaban kasa ba tun da babu wani daga kowanne yanki na siyasa da aka hana shi shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar. Abin da ke tabbatar da shiyyar shugaban kasa shi ne samar da shugaban jam’iyya.
Ya ce ga dukkan alamu mukamin shugabacin jam’iyya zai ci gaba da zama a Arewa ne kuma tikitin takarar shugaban kasa zai koma Kudu.
Dangane da ra’ayin cewa Gwamna Makinde ne zai kasance a matsayin dan takarar jam’iyyar a shekarar 2027, Dakta Pearse ya ce ana kallon Makinde a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2027.
“Ina ganin wannan hasashe ya samo asali ne daga yadda Makinde ya yi fice a matsayinsa na Gwamnan Jihar Oyo, da kyawawan halayensa, da jajircewarsa ga dimokuradiyya, da bin doka da oda. Yana gudanar da mulki ta hanyar sanya kowa da kowa. An gaya mini cewa ana kiransa “Seyi Masoyi.”
“Idan Makinde ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP kuma ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar, zai zama shugaban Nijeriya a 2027,” in ji Pearse.
Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na bukatar sauya alkibla daga gwamnatin APC mai cike da rudani. “Ba wata jam’iyyar siyasa da take tsarkakakkiya, amma idan aka kwatanta da APC, PDP mai daraja ce,” in ji Pearse.
Shi ma mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa Dr. Ibrahim Abdullahi yana da wannan ra’ayin. Kuma yana ganin Makinde zai iya zama dan siyasar PDP da za a fafata da shi.
A nasa jawabin, Abdullahi ya ce damar PDP a 2027 ya fi kowanne irin lokaci saboda rashin aikin da Tinubu da gwamnatin APC ke yi, wanda ke ci gaba da jawo wahalhalu da bacin rai a kasar nan.
“Idan aka yi la’akari da yadda al’amura ke gudana, za a iya mayar da takarar shugabancin kasarnan a 2027 zuwa Kudu-maso-Yamma cikin dabarar da PDP za ta iya cimma a tare bisa kyakkyawar cimma matsaya ta ‘yan Arewa kan wanda zai zama abokin takarar. Wannan domin gamsar da ra’ayoyin Kudu game da kididdigar yanki da addini bisa lura da yadda Tinubu ya amfana da wannan rarrabuwar.
“Da ma gwamna Seyi Makinde ya yi daidai da ainihin abin da PDP ke bukata a lissafin tikitin takarar shugaban kasa a 2027.
Sai dai kuma wani abin ban mamaki shi ne, har yanzu gwamnan bai nuna sha’awa ba, domin ga dukkan alamu ya shagaltu da ayyukan al’umma domin bunkasa zamantakewa da tattalin arzikinsu.
Yana daya daga cikin jiga-jigan gwamna mai aikin a zo a gani a wannan jamhuriyya. Ana auna shi a matsayin wanda yake da babbar dama wajen jan wannan ragama.
“Kasar nan tana cikin halin rugujewa da baganniya, tir da halin gwamnatin APC mara basira. Ya bayyana cewa suna kan turbar tukin da babu direba. Tabarbarewar hauhawar farashin kayayyaki yana hade ne da gazawar gudanarwa wajen mayar da Nijeriya kasa mafi muni a doron kasa wajen gudanar da rayuwa a cikinta,” in ji Abdullahi.
Sai dai Makinde ba bakon ba ne wajen shawo kan takaddamar siyasa kamar yadda ya yi a 2019, lokacin da ya kayar da ikon da ke jihar Oyo ya lashe zaben gwamna.
Jam’iyyar PDP a jihar Oyo kafin 2019 ta kwanta dama. Gabanin zaben 2019, babban jigon jam’iyyar, tsohon Gwamna Rashidi Ladoja, ya jefar da jam’iyyar ya koma jam’iyyar Accord Party saboda bai ji dadin yadda aka raba tsarin jam’iyyar ba.
Wata majiya mai tushe a siyasar jihar Oyo ta ce, “Na tuna a lokacin hatta dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga Ladoja da ya fice daga jam’iyyar, har ya kai ga shi (Atiku) ya kira Sakataren tsare-tsare na kasa na jam’iyyar a lokacin, Kanal Austin Akobundu mai ritaya (yanzu Sanata ne), da kuma shugaban jam’iyyar na lokacin, Prince Uche Secondus, cewa babu wani dalilin da zai sa Ladoja ya fice daga jam’iyyar.
“Ladoja ya bar jam’iyyar ne saura ‘yan watanni kafin zaben 2019, kuma wanda ya rage (cikin masu ruwa da tsaki) shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Seyi Makinde.
“Sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 ya nuna cewa PDP ta lashe jihar ga Atiku, kuma Seyi Makinde ne ya ci zaben gwamna da tazara mai yawa.
“Eh, kowa na iya cin zabe, amma maganar gaskiya, a Jihar Oyo a lokacin, Makinde ne ya yi ruwa ya yi tsaki, ya yaki gwamnati mai ci, tsofaffin gwamnonin biyu (Ladoja da Marigayi Alao Akala) wadanda dukkansu ke da bambancin ra’ayi, minista mai ci, kuma mafi muhimmanci, Gwamnatin Tarayya ta APC a tsakiya.
“Ya yi kokari ya iya kwace taura a hannun kuturu domin al’umma, sannan karfin ikon Allah yana tare da shi. Kafin shekarar 2019, Jam’iyyar ba ta da wakilci a dukkan fadin kasa, amma a zaben 2019, PDP ta lashe kujerun Gwamna, da Sanata, da kujeru biyar na Majalisar Tarayya, duk wadannan daga Jam’iyyar da aka yi wa lakabi da matattu,” inji majiyar. .
A yayin da PDP ke neman sabuwar alkibla kafin 2027, shin Makinde, wanda aka fi sani da tauraro mai haske na wato ‘PDP Star-Boy’ a turance, zai iya maimaita tarihi ta hanyar yin galaba a kan duk wani kalubale wajen kasancewa a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar? Amsar tana cikin watanni masu zuwa.