A watan Afrilun shekarar 2018, an gudanar da bikin murnar cika shekaru 30 da kafuwar yankin musamman na tattalin arziki na lardin Hainan a birnin Haiko, fardar lardin. Inda shugaban Xi ya sanar cewa, “Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ya yanke shawara cewa, zai goyi bayan gina yankin gwaji na cinikayya cikin ’yanci a dukkan tsibirin Hainan, kuma zai goyi bayan Hainan don bincike da inganta gina tashar cinikayya cikin ’yanci mai salon musamman na Sin a kai a kai, da kuma kafa manufofi da tsare-tsare na tashar cinikayya cikin ’yanci a matakai.”
’Yan jam’iyyar kwaminis ta Sin da marigayi Deng Xiaoping ya wakilta, sun mayar da budadden ra’ayinsu zuwa ra’ayin mulkin kasa wato “bude kofa ga kasashen waje”, kuma sun dauki hakan a matsayin wata babbar manufar Sin. Bayan da aka gabatar da shi a cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata, manufar bude kofa ga kasashen waje da Sin ta yi ta samu sakamako mai kyau.
- Yan Kasuwan Ketare Za Su Samu Sabbin Damammaki A Kasar Sin
- Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Samu Sakamako Mai Kyau A Rabin Farko Na Shekarar Bana
Tun daga shekarar 2012, Xi Jinping ya yi amfani da ra’ayinsa na kokarin koya da kuma mallakar fasahohi daga sauran kasashen waje, ya fitar da sabon ra’ayin “ci gaba ta hanyar bude kofa”. Ya ce, bude kofa da Sin ta yi wa kasashen waje ya shafi fanonni da bangarori daban daban, kamata ya yi a inganta gina sabon yanayi na bude kofofin bangarori daban daban.
A sabon zamanin da muke ciki, Sin ta yi kokarin hada kan sauran kasashen duniya wajen raya tattalin arziki, da kuma kokarin hada dukkannin karfin kasashen duniya wajen bude kofofinsu tare.
Saboda ya dauki ra’ayin bude kofa ga kasashen wajen domin kokarin koya da kuma mallakar fasahohi daga sauran kasashen waje, Xi Jinping ya gabatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. A wannan sabon zamani, shawarar nan ta yi ta tabbatar da ganin kasashe daban daban sun ci gajiya tare. Xi ya ce, “bude kofa ita ce muhimmin karfi na ci gaban wayewar kan bil’adama, kuma hanya ce da ake bi wajen ciyar da dukkan kasashen duniya gaba.”
Sabon yanayin samun nasara tare ta hadin gwiwar kasa da kasa da Xi Jinping ke jagoranta, ba ma kawai ya sanya JKS take jagorantar al’ummun Sinawa da su bude kofar kasar Sin ga duk duniya ba, har ma ya sa kaimi da kuma kuzari ga sauran kasashen duniya da su bude kofa da kuma neman ci gaba tare. (Safiyah Ma)