Bayan da Xi Jinping ya fara aiki a matsayin shugaban kasar Sin, ya yi amfani da shekaru 8 wajen ba da jagoranci ga dukkanin al’ummomin kasar Sin domin yin wani muhimmin aikin da ya janyo hankulan kasashen duniya, wato kawar da kangin talauci baki daya a duk fadin kasar Sin. Aikin da ya fitar da masu fama da talauci kimanin miliyan dari daya dake yankunan karkarar kasar Sin daga kangin talauci. Lamarin da ya kasance abin al’ajabi a duk fadin duniya.
Xi Jinping ya kan ce, jama’a su ne tushen kasa, in aka samu lafiyayyar al’umma, za a samu zaman lafiyar kasa baki daya. Hakan ya sa, shugaba Xi ya gabatar da ra’ayin “mai da muradun jama’a a gaban komai” domin neman bunkasuwar kasa. Ra’ayin ya kuma kasance bukatarsa a fannin tsara harkokin raya zamantakewar al’umma da tattalin arzikin kasa, kuma shi ne burin kasar Sin a lokacin da take zurfafa ayyukan yin kwaskwarima bisa dukkan fannoni a sabon zamani. Kamar yadda shugaba Xi ya bayyana,“Mun mai da bukatun al’umma na jin dadin zaman rayuwa a matsayin babban burinmu, da kuma ba da karin tallafi ga al’ummun kasar cikin yanayin adalci, bisa sakamakon da aka samu a fannin yin kwaskwarima da neman bunkasuwa.”
- IMF Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2024 Zuwa Kashi 5%
- Kotu Ta Dawo Da Shaibu A Matsayin Mataimakin Gwamnan Edo
Wannan ra’ayin neman bunkasuwa na “mai da muradun jama’a a gaban komai” da shugaba Xi ya gabatar, ba kawai ya yi bayani game da tambayar “Sabo da wadanne mutane ne muka yi kwaskwarima”, haka kuma, ya yi bayani ne game da tambayar “Za mu dogaro kan wadanne mutane ne domin yin kwaskwarima”. Xi Jinping ya ce, “Ya kamata mu tsaya tsayin daka wajen tsara manufofinmu bisa ka’idojin ko jama’a za su nuna goyon baya ko a’a, ko jama’a za su yarda ko a’a, ko jama’a za su ji dadi ko a’a.
Kana, ya kamata mu bi ra’ayin al’umma, da girmama bukatunsu, da mai da hankali kan halayen da suke ciki, da kuma dukufa wajen kyautata zaman rayuwar al’umma. Ma’anar ita ce, a gabatar da kuma aiwatar da manufofi masu dacewa, domin ba ga jagoranci ga jama’ar kasa wajen neman ci gaba, yayin da muke samun karfin ci gaba da ayyukanmu bisa bunkatun da jama’ar kasa suke nunawa domin neman bunkasuwa.” (Mai Fassara: Maryam Yang)