Shafi ne da yake zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma, ciki sun haɗar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da lokaci, wanda shafin ya ji ta bakin mabiyansa game da wannan batu; “Mene ne lokaci?, Ta ya ya ake amfani da lokaci?, Fad’i muhimmancin lokaci da aka sani”.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor graphics) Kano:
Lokaci abu mai muhimmanci a rayuwar ɗan’adam. Ana amfani da lokaci wajen karatu, aiki, komai yana ɗauke da lokaci gaskiya. Komai da lokaci yake tafiya, ita kanta rayuwar ta lokacin komai ya tattara akan lokaci. Ai mutum ya yi amfani da lokacinsa wajen gina rayuwa mai inganci da aikin alheri shi ne ribar lokaci.
Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk
Lokaci wani abu ne da yake nuna yanayi a kodayaushe, sannan yake bada damar aiwatar da abubuwa masu kyau da mararsa kyau a rayuwa. Haka kuma yanayi ne da yake bada damar rayuwa a cikin daƙiƙu, mintuna, da kuma, awowi, ranaku, makonni dakuma shekaru. Ana amfani da lokaci ne ta hanyar da ya kamata kamar gudanar da rayuwa maikyau da zamantakewar yau da gobe, da kuma hanyoyin da ya dace na gudanar da rayuwa. Lokaci na yana da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da rayuwa. Amfanin lokaci na nufin amfani da lokaci ko kuma yadda ake amfani da shi wajen cimma burin mutum ko gudanar da ayyuka. Ga wasu daga cikin amfanin lokaci; inganta ayyuka, tsara ayyuka, kare lafiya, cimma burin rayuwa, inganta kwarewa, rage damuwa, ƙara hada kai, ƙarfafa jin daɗi, kula da al’amura, gina gaskiya. Yin amfani da shi a lokacin da ya dace, domin tabbatar da cigaban rayuwa, da kuma samun nasara a rayuwa.
Sunana Fadila Lamoɗo daga Jihar Kaduna:
Lokaci yana da matuƙar daraja, domin shi baya jira sai dai a jira shi. Idan ya tafi ya tafi kenan har abada sai dai a jira wani lokacin ba waccen na baya ba. Waɗanda suke wasa da lokaci so da dama ba sa fargaba sai wasu damarmaki sun tsere masu har abada. Waɗanda suke ƙoƙarin tsara lokacinsu kuma su kiyaye su, so da dama suna cin ribar lokacinsu domin shi zaɓen lokaci adana lokaci ne.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jahar Jigawa:
To, haƙiƙa lokaci wani abu ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwa, domin dukkaninta rayuwa tana gudana ne da lokaci, tunda lokaci shi ke kawo canji kowane iri a rayuwar al’umma.To, amfani da lokaci dole ne a wajen dukkanin ɗan’adam, domin lokaci ana amfani da shi ne wajen gudanar da dukkanin wani al’amari na rayuwa, kuma yana kasancewa wani ma’auni na faruwar al’amari ko akasin sa, lokaci shi ne ke jagorancin rayuwar al’umma. To, haƙiƙanin gaskiya muhimmancin lokaci a wajen ɗan’adam ya fi gaban ƙirdado ko ƙidayawa, domin dukkanin wani muhimmin al’amari na rayuwa yana gudana ne da lokaci. Don haka wanda ya yi amfani da lokaci yadda ya dace, sai ka ga ya yi nasara dukkanin al’amarinsa. To, shawarata a nan ita ce ya kamata mu sani lokaci wani abu ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwa, kuma idan ya wuce baya dawo wa. Don haka ya.kamata mutum ya yi amfani da shi yadda ya dace, domin gudun kaucewa da-na-sani a rayuwa.
Sunana Aisha T. Bello, daga Kaduna:
Lokaci na nufin ma’auni da ke shuɗewa tun daga dare zuwa safiya. Ana amfani da lokaci ne yadda ya dace, domin gundanar da rayuwar yau da kullum. Lokaci na da matuƙar muhimmanci ga ɗan’adam domin ana amfani da shi ne yadda ya dace da gunadar da ayyuka kamar ibada, karatu da sauran ayyuka na yau da kullum. Ya kamata mutane su riƙa ba lokaci muhimmanci musamman don gudanar da ayyukan alkhairi, musamman duba da yanayin rayuwa lokaci na gudu. Sai an kiyaye a tsara shi yadda ya dace kafin ya shuɗe, kar a bari a riƙa asarar lokaci a banza.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano LGA:
Wani abu ne da ubangijinmu yake bamu shi, domin taimakawa kawunanmu a nan duniya da kuma lahira. Kamar yadda shi kansa Allah subahanahu wata’ala ya kawo suratul asar. Ta yadda za mu yi aiki da lokacinmu shi ne; Muna yi wa Allah ibada daidai yadda za mu iya, domin kowannenmu ya sani duk ‘second’ idan ya wuce to, fa ba zai dawo ba. Haka ma wajen neman ilmi ko abin duniya, to mu yi amfani da wannan lokacin kafin ya wuce mu. Muhimmancinsa shi ne mu sani cewa, kamar yadda kowa ya san cewa idan an mutu ba a dawowa, to, haka shi ma lokacin yake. Don haka mu daure mu yi aiki da lokacinmu wajen gina gobenmu. Shawarata a nan ita ce, kada mutum ya ga ya sami lokaci ya bar shi ya wuce haka sa-ka-ka. Domin idan ma ba mu yi aiki da shi ba a wannan lokacin, to, akwai da-na-sani a nan duniya, ko a ranar gobe kiyama. Allah ya sa mu dace, amin.
Sunana Tasleem Adam, Jihar Bauchi:
Lokaci na ɓangaren rayuwar mu da ya shafi mu’amala, dangantaka, da ayyuka tare da wasu mutane. Shiryawa da rarraba lokaci don ayyukan zamantakewa, kamar tarurruka, ko bukukuwa. Rarraba lokaci don kula da dangantaka da iyali da abokai. Sadaukar da lokaci don halartar abubuwan da suka faru kamar; bikin aure, ranar haihuwa, ko kaɗe-kaɗe don yin zamantakewa da wasu. Yin amfani da lokaci a kan dandamalin sada zumunta don yin mu’amala da wasu, raba kwarewa, da kasancewa a cikin hulɗa. Raba lokaci tare da abokan aiki ko abokai ya yin hutu a wurin aiki ko makaranta don yin mu’amala da kuma samun kuzari. Lokaci na taimakawa wajen gina da kuma ƙulla kyakkyawar dangantaka da wasu.
Sunan Ibrahim Garba Bizi, Damaturu, Jihar Yobe:
Lokaci shi ne tsarin da ake amfani da shi wajen auna tsawon rayuwa, ayyuka, da abubuwan da ke faruwa a duniya daga wata daƙiƙa zuwa wata. Akan yi amfani da lokaci wajen tsara ayyuka, gudanar da al’amura cikin tsari, da cimma manufofi cikin taƙaitaccen lokaci. Lokaci yana da muhimmanci domin yana taimakawa wajen kaucewa bata lokaci, samun nasara a rayuwa, da kuma gudanar da rayuwa cikin tsari. A al’umma su riƙa daraja lokaci, su guji ɓata shi, su kuma koya wa yara yadda za su yi amfani da lokaci wajen inganta rayuwarsu da ta ƙasa.
Sunana Princess Fatima Mazadu, Jihar Gombe:
Da farko dai a sanina lokaci shi ne jigon aiki da komai na rayuwa, in kana raye ka ke da lokaci in ka mutu wasu za su ci gaba da morar lokacin. Lokaci abu ne mai muhimmanci na rayuwa, ako wani ɓangare sai da lokaci ake komai. Ta daidaita lamura da ayyuka ba tare da ƙetare wa ba, saboda muhimmancin lokaci. Ibada, aiki na hannu jiki, kwakwalwa, karatu. Adinga girmama lokaci wurin ibada da bautar Allah, a kiyaye sosai, karatu, sana’a, ta hannu ko ta ƙarfi. A kula da ayyuka akan lokaci ayi amfani da lokaci dan watarana lokacin zai wuce har abada baka tanadi komai ba, gashi loakci in ya wuce ba dawuwa har abada bature ya ce “time is precious”.
Sunana Muktari Sabo, Jahun A Jahar Jigawa:
Lokaci wata dama ce da Allah yake bawa halittarsa don rayuwarsu da kuma abin da za su gudanar a cikin rayuwar bakiɗaya. Ana amfani da lokaci ne ta hanyoyi da dama, ko dai a yi amfani da shi ta hanya mai kyau, ko akasin haka. Ko kuma a bar shi ya tafi haka ba tare da an yi amfani da shi ba. Haƙiƙa lokaci yana da muhimmanci sosai, don muhimmancinsa Allah subhanahu wata’ala har rantsuwa ya yi da shi, kuma yana daga muhimmancin lokaci kayi amfani da shi ta hanya mafi kyau. Babu shakka ya kamata mutane mu riƙa amfani da lokaci ta hanya mafi kyau, domin shi lokaci wucewa yake ko kayi amfani da shi ko ba ka yi ba, ko ta hanya mai kyau ko akasin haka, kuma in ya wuce, ya wuce kenan.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Naija:
Lokaci shi ne wanda za ka kira mutu oo a waya ko wani ɓangare na daban ka ce kana son ganin mutum, ya ce Zaire baka lokacin da za ka je ko shi ya je. Yadda ake amfani da lokaci shi ne; idan an baka lokaci kar ka saɓa lokacin da aka ce ka je. Fa’idar lokaci wasu ba sa ɗaukar lokaci da mahimmanci sai sun gota lokaci, to, ya zamana ana bin ƙa’idar lokaci.
Sunana Idris Haruna Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Lokaci na nufin wani tsari ko ma’auni da ake amfani da shi domin auna tsawon lokacin da wani abu ke faruwa, ko don sanin yaushe wani abu zai faru ko ya faru a baya. Misali; Lokaci na nuni da safe, rana, yamma, dare, ko kuma mintuna da awanni. Ana amfani da lokaci ta hanyoyi da dama, ciki har da; Tsara Ayyuka, kamar lokutan zuwa makaranta, aiki, ko ibada. Kiyasta tsawon wani aiki, misali; aikin da zai ɗauki awa ɗaya. Tantance tarihi, Kamar; lokacin haihuwa ko wani babban lamari. Gudanar da rayuwa; Domin yin komai a lokacin da ya dace, ba tare da ɓata lokaci ba. Lokaci yana da matuƙar muhimmanci saboda rayuwa tana tafiya da lokaci, duk abin da muke yi na buƙatar lokaci. Ba za a iya mayar da lokaci ba idan ya wuce, ya wuce har abada. Yana taimaka wa mutum ya cimma buri, idan ya tsara lokacinsa da kyau. Yana hana ɓata lokaci a banza yana koyar da tsafta da daidaito a rayuwa. Shawarata ita ce: Al’umma su koyi darajar lokaci, su guji ɓata shi, su kuma koya wa yara tun daga ƙuruciya yadda za su tsara lokacinsu. A gina al’umma mai ɗorewa da cigaba ta hanyar kiyaye lokaci a kowane fanni; ilimi, sana’a, ibada, da hulɗar yau da kullum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp