A kokarinta na fara shirye-shirye gudanar da zabe da wuri, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa tuni ta raba kashi 50 na kayayyakin zabe.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayyana haka lokacin da tawaga ta musamman da ke saka ido kan zabe na kungiyar Afirka ta ziyarce shi, inda ya jaddada gwarin gwiwar hukumar na gudanar da sahihin zabe.
- Zan Bayyana Dan Takarar Da Zan Mara Wa Baya A Janairu – Wike
- Qatar 2022: Babban Bankin Argentina Na Kokarin Sanya Hoton Messi A Takardun Kudin Kasar
Yakubu ya kara da cewa duk da irin kalubalen da hukumar take fuskanta za ta gudanar da sahihin zabe.
Ya ce, “A cikin makonni uku, an kone mana ofishoshi har guda uku a sassa daban-daban na kasar nan. A dukkan wadannan farmaki ba a samu asarar rai ba, amma an kone mana kayayyaki zabe.
“Za dai mu iya dawo da kayayyakin da suka kone, amma ya kamata a dakatar da wannan lamari.
“Ina mai tabbatar da cewa za mu shan ‘yar karamar wahala, amma dai za mu dawo da kayayyakin da muka rasa kuma wannan bai hana hukumar ta gudanar da sahihin zabe kamar yadda doka ta dora mana. Sannan babu gudu babu ja da baya wajen yin amfani da naurar bayyana sakamakon zabe.”
Duk da kiraye-kirayen al’umma na kara wa’adin yin rajistar zabe, amma hukumar da ce hakan zai shafi tsare-tsarenta matukar ta kara wa’adin yin rajista, wanda ta ce tana son kammala duk wasu shiryde-shirye kafin zaben 2023.
Sai dai kuma a wannan makon, shugaban INEC ya fito karara ya bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare a ofisoshin INEC babbar barazana ce da ke fuskantar zaben 2023.
Ya dai amince cewa hukumar na iya dawo da wasu muhimman kayayyaki da suka kone amma idan har an dakatar da hare-haren, saboda ci gaba da kone-konen zai iya shafar sababbin kayayyaki da hukumar take rabawa.
Yakubu ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin wucin-gadi da ke binciken farmakin kan ofisoshin INEC na majalisar wakilai a Abuja.
Kwamitin ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda ofishin ministan shari’a ke cewa har yanzu bai samu bukata ko guda daya ba na hukunta wadanda suke kai wannan harin.
Yakubu ya ce, “Muna kokarin ci gaba da shirye-shiryenmu na gudanar da zaben 2023. A yanzu dai muna kokarin dawo da dukkan kayayyakinmu ko neman wata hanya ta daban. A halin yanzu dai idan wannan farmaki ya ci gaba da gudana, zai yi wa hukumar wahala da murmure a kan lokaci kafin zaben 2023. Idan har an dakatar da farmakin, to za mu iya murmurewa, amma dai idan har farmakin ya ci gaba da faruwa, zai yi wa hukumar wahala ta murmure. Wannan shi ya sa muke kokarin a dakatar da farmakin wanda ya zama wajibi mu gudanar da wannan sauraron ra’ayi ta yadda za a samu sakamako mai kyau.
“Farmakin ya fara illa ga shirye-shiryen zaben 2023. Abu na farko shi ne, kayayyakin da suka kone musamman ma ofisoshi za su dauki lokaci kafin a iya gyarawa. Su ba kamar bayanai ba ne da za a iya bayarwa daga na’ura. Domin haka, dole a dauki wasu shirye-shiryen na daban. A wasu jihohin da farmakin ya fi zafi, dole mu shirya daukar haya. Ya zama wajibi a wasu wurare mu dauki hayar kayayyaki. A kuma wasu yankunan, ba za mu iya samun hayar kayayyakin ba, wannan ne ta sa dole mu duba wata hanyar kan lalata mana kayayyaki.
“Na biyu, mun rasa kayyaki masu yawa wanda akwai bukatar sake dawo da su. Alal misali a farmakin kwanan nan, mun tafka asarar katinan zabe masu yawa. A kan katin zabe, muna iya dawo da su ta hanyar tura bukata ga babban ofishinmu da ke jiha wajen sake bugawa. Wannan cikin sauki za mu iya dawo da su kuma har a sake bugawa.
“Dole ne hukumar ta ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro wajen tsare kayayyakin, kamar yadda na fadi tun a farko akwai matukar kalubale, amma jami’an tsaro za su tsare mu da sauran kayayyakin kasa. Saboda haka, wannan farmaki da ake kai wa ofisoshinmu babban kalubale ne ga jami’an tsaronmu wanda na san za su iya dakatar da shi.
“A yanzu haka dole mu sake gina ofisoshinmu da aka kone kuma muna da abubuwa da yawa da za mu yi da kudadenmu. Ba za mu ci gaba da tsayawa kan gina ofisoshin ba kawai. Farmakin da ya fi mana muni shi ne na karamar hukumar Izzi da ke Jihar Ebonyi. An dai fara kai farmaki ne a ofishin a ranar 18 ga watan Mayun 2012. Mun gyara ofishin inda jami’anmu suka koma a Juma’a. Amma a ranar Lahadin wannan mako aka sake kona ofishin kurmus da wasu guda biyar wanda hakan ya karya gwarin gwimar da muke da ita. Akwai ofisoshi guda biyar wanda koma mun sake gyarawa sai an kara konawa.”
Da yake karin haske kan yadda har yanzu ba a hukunta ko mutum daya ba dangane da wannan laifi ba, mataimakin darakta a ofishin ministan shari’a, Yusuf Abdullahi ya bayyana wa ‘yan majalisar cewa har yanzu babu bukata a kan hakan.
Ya ce, “Ofishin ministan shari’a shi ne ke da hurumin gurfanar da masu laifi lokacin da jami’an tsaro suka tura musu. Idan an tura mana kara na gurfanarwa, nan take za mu tattauna tare da yin abin da ya dace na kamawa da kuma gurfanar da wadanda suke kone ofishoshin INEC, kamar yadda aikin ofishinmu ya kunsa har yanzu ba mu sami bukatar kan gurfanar da wani ba. Wannan yana cikin wasikarmu, a daidai lokacin da muka samu bukata a kan ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga ko masu kone ofisoshin INCE, nan take za mu dauki mataki na tabbatar da cewa mun bin tsarin doka wajen yin nazari da bayar da shaida da kuma gurfanar da wadanda ake zargi.”
Babu Dalilin Da Zai Sa INEC Ta Gaza Gudanar Da Sahihin Zabe – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada aniyarsa na tabbatar da sahihin zabe a 2023 da zai kasance mafi karbuwa a wurin al’ummar kasar nan.
A cikin sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin yada labarai, Garba Shehu ya fitar a Abuja, ta bayyana cewa shugaban kasa ya fadi hakan ne a Washington DC da ke Kasar Amurka lokacin da yake jawabi.
“INEC ta shirya, saboda sai da na tabbatar na ba su dukkan kuadaden da suke bukata, domin ban san wani uzuri na cewa gwamnati ta hana su kudaden da suke bukata,” in ji Shugaba Buhari lokacin da yake amsa tambayoyi game da zabe.
Ya kara da cewa, “Tun daga 2015, zabenmu ke kara samun ingantuwa. A zaben 2019 da sauran zabukan cike gurbi da zabukan da aka yi a jihohin Edo, Ekiti, Anambra da kuma Osun sun nuna yadda ake samun ci gaba a harkokin zabe a Nijeriya.
“Wannan ne ya sa muke da kwarin gwiwa a zaben 2023. Ta hanyar masu sa ido na kasa da kasa za a samu sahihin zabe da zai kasance karbabbe ga koma.”
Sau 50 Ana Kone Ofishoshin INEC Cikin Shekaru 4
Binciken LEADERSHIP ya tabbatar da cewa an kone ofishoshin INEC har sau 50 a tsakanin 20219 zuwa 2022.
Sakataren yada labaran INEC, Mista Rotimi Oyekanmi shi ya bayyana wa LEADERSHIP hakan a Abuja a cikin rahoto mai taken ‘jaddawalin farmakin da aka kai wa ofisoshin INEC a tsakanin 2029 zuwa ranar 12 ga watan Disambar 2022.’
“Farmakin sun faru ne sakamakon rikice-rikicen zabe da haramtattun zanga-zangar da ba su da alaka da zabe da ayyukan ‘yan daba da kuma na ‘yan bindiga.
“Wannan jaddawali bai hada da kayayyakin da suka lalace ba sakamakon gobara da tsararruka kamar irinsu ambaliyar ruwa ta mamaye da sacewa ko lalata kayayyakin zabe lokacin zabe da jami’anmu da aka farmaka a lokacin gudanar da ayyukansu,” in ji Oyekanmi.
Binciken a kan lamarin ya nuna cewa jihohi 15 cikin 36 na kasar nan ne aka kai wadaddan farmaki.
Dukkan jihohin da aka kai wannan farmaki a yankin kudu maso yamma sun hada da Ebonyi, Inugu, Abiya, Imo da kuma Anambra. Sauran jihohin su ne Kuros Ribas, Akwa Ibom, Bayelsa, Ondo, Legas, Ogun da kuma Osun.
A cewar rahoton, lamarin dai sun hada da alaka da ‘yan bindiga, rikice-rikicen bayan zabe, Boko Haram, ayyukan ‘yan daba lokacin zabe, zanga-zangar EndSARS, ‘yan bindigar da ba a sani ba da kuma ayyukan ‘yan ta’adda.
Yanayin farmakin sun hada da kone-kone har guda 20 da lalatawa guda 26 da kuma konawa tare da lalatawa guda hudu.
Rahoton ya ruwaito cewa an farmaki ofisoshin INEC har guda takwas a 2018, an samu guda 22 a 2020, sannan an samu 12 a 2021, inda aka samu farmaki guda takwas a 2022.
INEC Ta Rattaba Hannun YarjejeniYa Da Kungiyoyin Sufuri Domin Jigilar Kayyyakin Zabe
Gabanin zaben 2023, a ranar Talata da ta gabata ce hukumar zabe ta rattaba hannun yarjejeniya da kungiyoyin sufuri, domin yin jigilar jami’anta da kuma kayayyakin zabe a fadin kasar nan.
Yarjejeniyar ta kunshi kungiyar sufuri ta ruwa wanda za ta taimaka wa hukumar wajen tsallakawa da jami’anta da kayayyakin zabe ta ruwa.
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, “Mun dauki darasi kan abubuwan da suka faru a baya, domin haka ina bukatar dukkan kungiyoyin sufuri su rattaba hannu kan wannan yarjejeniya.
“Muna ganin irin gudummuwar da kuke bayarwa a kasa, domin haka ku tabbatar da cewa kun bayar da gudummuwa kan ci gaban kasa a daidai lokacin da hukumar ta makara wajen daukar wata hanya ta daban.
“Ya kamata kungiyoyin sufuri su kula da mambobinsu wajen tabbatar da sun dauki jami’anmu da kayayyakin zabe a wurin da ake bukata, sannan kuma su tabbatar sun dawo da su bayan an kammala zabe. Kwangilarku ta kasance zuwa da dawowa wurin jigilar jami’anmu da kayayyakin zabe.
“Zaben 2023 ya kasance zai gudana ne a dukkan fadin kasar nan wanda jami’ai miliyan daya za su yi aikin tare da jigilar kayayyakin zabe cikin makonni biyu daga ofisoshinmu da ke kananan hukumomin 774, a gundumomi 8,809 da mazabu 176,846 da ke fadin kasarmu.
“Muna bukatar motoci 100,000 da kwalekwale 4,200 irin na rundunar sojojin ruwan Nijeriya. Muna bukatar su ne gabanin kwanaki 66 da za su bai wa ‘yan Nijeriya damar yin zabe cikin salama.”
Yakubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya za a fara tun daga karfe 8.30 na safe a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023 na shugaban kasa da na ‘yan majalisar, sannan a ranar Asabar 11 ga watan Maris ta 2023 za a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jiha a duk fadin Nijeriya.