Alamu na nuni da cewa, farashin man fetur na daf da tashi yayin da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya amince da tarin bashi a kansa.
A makwanni biyu da suka gabata ne dai jami’an gwamnati suka yi ta tsokaci kan yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa kan dala, hakan ta sa, masu hasashe ke ganin cewa, farashin man fetur na Naira 617 a hukumance ba zai dore ba.
- ACF Ta Yaba Wa Tinubu Kan Amincewa Da Ziyarar Sulhu Da Shugaban Sojojin Nijeriya Ya Kai A Nijar
- Batun Tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya Guda 11
A makonnin da suka gabata, an ga dogayen layukan man fetur sun sake kunno kai a galibin gidajen mai na ‘yan kasuwa masu zaman kansu a Abuja, Legas da sauran jihohi da dama a fadin kasar nan, inda ake sayar da fetur din a kusan Naira 720 kan kowace lita, wasu kuma kan Naira 1,000 a kowace lita.
Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a shekarar da ta gabata bayan bayyana cire tallafin man da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.