Shin kun san, a lokacin da Sinawa suka hadu da juna, gaisuwar da suke yi ita ce, “Shin ka ci abinci?” Wannan gaisuwa mai sauki tana nuna damuwar mutanen dake rayuwa bisa aikin noma, wato ma’ana, tambaya ce a kan ko ana da isasshen abinci?
A halin yanzu, wannan gaisuwa mai cike da nuna damuwa, tana samun sauyi mai ban sha’awa a yankunan karkarar kasar Sin. Dai Yihui, wadda ba ta wuce shekaru 30 da haihuwa ba, ta koma garinta na lardin Jiangsu, domin kula da gandun noma na iyalinta, inda ta yi kokarin kara yawan amfanin gona da kashi 35 bisa dari ta hanyar amfani da injunan noma na fasahar zamani, sai dai kuma mazauna garin sun canza gaisuwar gargajiya da ake yi daga “Shin kin ci abinci” zuwa “Yaya rayuwarki a garin?” Wannan gaisuwa ta nuna yadda irin gagaruman sauye-sauye da tsarin farfado da karkara a dukkan fannoni da ake kawo wa jama’ar kasar Sin.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp