Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Najeriya da Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ba da kyautar gida ga daya daga cikin jami’an dake gadi mafi dadewa a jami’o’in biyu, Malam Umar Mohammed Sanda bisa gaskiyarsa da rikon amana
Da yake gabatar da makullan gidan ga Malam Sanda a ranar Laraba 21 ga watan Yuni, 2023 a muhallin jami’ar MAAUN na dindindin, Farfesa Gwarzo ya ce Malam Sanda ya yi aiki a Jami’o’in Nijar da Nijeriya sama da shekaru goma, kuma an same shi da gaskiya da rikon amana a duk tsawon lokacin
A madadin jami’ar MAAUN na Nijar da Nijeriya, ina so na ba da wannan ladan gidan nan gare ka saboda gaskiya da rikon amanarka
Na yanke shawarar ba shi gida ne domin ya samu wurin da zai zauna da iyalinsa cikin kwanciyar hankali
Nayi shawarar bashi wani abu mai daraja saboda mutum ne mai himma wanda a kodayaushe yake kula da ayyukansa kuma ya kan tsaya a inda na nemi ya tsaya,” Farfesa Gwarzo ya ce a yayin da yake gabatar da makullan gidan ga Malam Sanda
A don haka ya shawarci wanda aka bai wa gidan da ya ci gaba da kasancewa mai gaskiya da rikon amana da kuma aiki tukuru a duk inda ya samu kansa
Farfesa Gwarzo ya kuma bukaci sauran ma’aikatan da ke aiki a Jami’ar da sauran wurare da su yi koyi da Malam Sanda domin a cewarsa gaskiya da rikon amana tana biya
Da yake mayar da jawabi, Malam Sanda ya nuna jin dadinsa ga Jami’ar da kuma wanda ya kafa jami’ar bisa wannan gagarumin aiki tare da addu’ar Allah ya saka masa da alheri