Mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere, Farfesa Umar Pate, ya gargadi ‘yan jaridun da ke aikin aika rahotanni da yin taka-tsantsan da nufin guje wa haifar da rikici a tsakanin al’umma.
Ferfesa Pate ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da lacca mai take ‘kafofin sadarwa da tsaron kasa’ a Yola, a lokacin bukin Karrama fitattun mutane da kafar sadarwar TGNews ta gudanar.
- Ashirye Muke Mu Amsa Duk Kura-kuran Da ‘Yan Jarida Suka Gano A Gwamnatinmu – Tinubu
- 2027: Atiku, Kwankwaso Da Obi Na Shirin Kafa Babbar Jam’iyyar Adawa – Pat Utomi
Ya ce yin amfani da jita-jita da karairayi masu hadari na haifar da yanayin da zai tarwatsa kan al’umma.
Farfesa Pate ya kasance kwararren dan jarida kuma kwararren masanin harkar sadarwa a duniya, ya ce amintacce, gaskiya, da kuzari su ne alamomin cikar ka’idodin aikin jarida mai inganci.
Ya ce bai kamata a dunga aika rahotanninn karya ga jama’a ba, abu ne da ke canza tunanin mutane zuwa wani abu daban, musamman kan halin da ake ciki.
Farfesa Pate ya shawarci ‘yan jaridu da kada su bari kalubalen da ke tattare da bullowar yanar gizo da kuma juyin juya halin fasahar sadarwar ta hana su ci gaba da bin ka’idojin aiki.