Shugaban masanan sararin samaniya na kasar Indiya ya tabbatar da cewa, baraguzen wata babbar rokar tauraron dan Adam ce ta fado a gabar tekun kasar Australiya wacce za ta iya kasancewa ta kasar Indiya ko kuma akasin hakan.
“Ba za mu iya tabbatar da cewa ba namu ba ne sai mun tantance shi,” masani S Somanath ya shaida wa BBC.
An yi ta cece-kuce game da baraguzen tun lokacin da aka gano shi a bakin tekun Green Head, kimanin kilomita 250 daga arewacin Perth na Australiya a karshen makon da ya gabata.
Wasu da yawa sun yi zargin cewa, yana iya kasancewa daga sabon tauraron duniyar wata ne na Indiya da ta harba a ranar Juma’ar da ta gabata amma masana sararin samaniyar Indiya cikin gaggawa suka yi fatali da wannan zargin.
Baraguzen mai fadin mita 2.5 da kuma tsayi 2.5 zuwa 3, ya haifar da fargaba sosai a tsakanin mazauna bakin tekun Green Head.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp