Gwamnatin jihar Adamawa ta sake duba dokar hana fita data sanya ta tsawon sa’o’i 24 a fadin jihar bayan wasu matasa sun afka rumbun ajiyar Abincin Jihar sun wawure kayan abinci a ma’ajiyar gwamnati da ke Yola, babban birnin jihar.
Yanzu haka dokar za ta fara aiki ne daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe daga ranar Litinin dinnan don baiwa mutane damar ci gaba da gudanar da harkokinsu.
- Fintiri Ya Sanya Dokar Hana fita Awa 24 A Adamawa
- Mutum 5 Sun Mutu Lokacin Fasa Rumbun Adanan Abinci A Adamawa
Gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce kara yawan jami’an tsaro zai tabbatar da bin wannan umarni da kuma ci gaba da wanzar da zaman lafiya a fadin Jihar.
“Mun dauki matakin sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka sanya a kananan hukumomi 21 na jihar Adamawa, yanzu dokar za ta fara daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe, an kuma kara inganta tsaro a fadin Jihar. Cewar gwamna Fintiri.