Kwanturolan Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Ƙasa (NIS), reshen Jihar Ribas, CIS Sunday James ya bayyana cewa fasahar zane-zane na ɗaya daga cikin sana’o’in da za su ƙara bunƙasa samar wa Nijeriya da kuɗaɗen shiga daga waje matuƙar an mayar da hankali a kai.
Kwanturolan ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci wata cibiyar baje kolin hotuna da zane-zane ta Moriri da ke Jihar Ribas.
Da yake jawabi, CIS Sunday ya ƙarfafa gwiwar mai cibiyar a kan yadda zai fadada cibiyar da buɗe ƙofarta ga mutane tare da gudanar da kasuwancin hotunan zuwa ƙasashen waje ta yadda zai samu ƙarin kudaden shiga daga waje.
Ya ƙara da cewa, zane-zane na kayan al’adu da fasahohi na Nijeriya suna da asali da tarihi ba a Afirka kaɗai ba har da ƙasashen waje, don haka za su samu karɓuwa sosai idan aka fara yin safararsu zuwa ƙetare.
Cibiyar zane-zanen wacce take katafaren bene mai hawa biyu, ta ƙunshi zane-zane da hotuna da ƙwararru suka samar masu ƙayatarwa.
Shugaban cibiyar, Kayode Adeoti ya samar da cibiyar ta Mariri ce a yayin da ake fama da Annobar COVID-19, inda ta bai wa ƙwararru damar zuwa su baje kolin fasaharsu ta zane-zane.