An gudanar da taron shirin matsugunnan bil Adama na MDD wato UN-HABITAT karo na biyu a birnin Nairobin kasar Kenya, tsakanin ranaikun 5 zuwa 9 ga wannan wata na Yuni, taron da ya maida hankali ga batutuwan da suka shafi yanayin birane, da tinkarar rikicin birane da sauransu.
Tuni dai kasar Sin ta ingiza more fasahohi a fannin samun bunkasuwa mai dorewa a birane da kauyukan kasashen Afirka, wanda hakan ya samar da tunani, da shirye-shiryen Sin ga kasashen Afirka, a fannonin inganta yanayin zaman rayuwar dan Adam.
A watan Janairu na shekarar bana, an fara zirga-zirgar jiragen kasa, a mataki na farko na aikin gina hanyoyin jiragen kasa na jihar Lagos dake tarayyar Nijeriya, aikin da kamfanin gine-gine na kasar Sin ya dauki alhakin gudanarwa. Wannan ce dai hanya ta farko da kamfanin Sin ya tsara, da kuma ginawa da kansa a yammacin Afirka.
Da yake tsokaci game da hakan, jami’in hukumar sufuri a jihar Lagos Babatunde Odejide, ya bayyana cewa, aikin ya saukakawa jama’ar dake wurin zirga-zirga. Kana jiragen kasan na amfani ne da wutar lantarki, matakin da ya rage fitar da iska mai gurbata muhalli.
Shi kuwa a nasa tsokaci game da wannan batu, farfesa a jami’ar Addis Ababa ta kasar Habasha Costantinos Berhutesfa, cewa ya yi idan kasashen Afirka suka yi hadin gwiwa tare da kasar Sin, ba ma kawai za a yi amfani da albarkatun makamashi na Afirka ba tare da gurbata muhalli ba ne kadai, matakin zai kuma ingiza damar more fasahohi, da nasarori da kasashen Afirka ke ci, a fannin amfani da makamashi mai tsafta. (Zainab)