Biyo bayan wata mummunar fashewar tankar man fetur da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 100 a daren ranar Talata a jihar Jigawa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya sanar da daukar matakin gaggawa na gwamnatin tarayya tare da yin kira da a sake duba ka’idojin tsaron sufurin man fetur a fadin Nijeriya.
Mataimakin shugaban kasar, a madadin shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana alhininsa na musamman ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba su ikon jure wannan rashi.
A cikin sakon ta’aziyyar da ya aike a ranar Laraba, Shettima, a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce, “Na Kadu sosai da samun wannan mummunan labari.”
Lamarin wanda ya afku a kauyen Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, ya jefa al’ummar Nijeriya baki daya cikin alhini.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayar da umarnin tura jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA cikin gaggawa zuwa jihar Jigawa.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma yabawa jami’an kiwon lafiya da suka isa wurin da gaggawa bisa namijin kokarin da suka yi, inda ya bayyana sadaukarwar da suka yi da cewa, “Wannan shi ne halin da ‘yan Nijeriya suka yi fice da shi.”