Fashewar tukunyar gas a wani kantin sayar da gas ta yi sanadin kone shaguna tare da raunata mutane 20 a Kano.
Lamarin ya faru a unguwar Sheka Karshen Kwalta, unguwa ce mai cike da hada-hadar jama’a a Kano.
- Wata Yarinya ‘Yar Shekaru 4 Ta Mutu Bayan Ta Faɗa Rijiya A Kano
- Badakalar Kudade: EFCC Ta Sako Dakataccen AKanta-Janar, Ahmed Idris
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar Alhamis, inda wata tukunyar gas ta fashe kuma nan take ta kama da wuta.
Gobarar ta lalata wurin da wasu shaguna kusan uku da ke kusa, ciki har da wani bangare na wani gida da ke daura da shagon.
Shaidu sun shaida da cewa, sun ji karar fashewar tukunyar mai dauke da iskar gas a ciki.
Wani ganau mai suna, Malam Abubakar, ya ce an garzaya da mutane da dama zuwa asibiti tsirara saboda duk fatar jikinsu ta kone-kone.
Ya ce sama da wasu mutane 10 da lamarin ya rutsa da su, akasari wadanda ke cikin shagon ne da kuma mutanen da ke kusa da wurin da suke sana’arsu.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce mutane 20 ne amarin ya shafa amma an ceto su da ransu, kuma yanzu haka suna samun kulawa a asibitoci.
Yusif ya ce lamarin ya faru ne sakamakon amfani da wuta da wani mutum mai soya kifi a kusa da shagon gas a wurin.