Fasinjoji da dama sun jikkata sanadiyyar karo da motocin haya na bas biyu suka yi a jihar Legas.
Hatsarin wanda ya auku a ranar Talata, ya faru ne da safiyar ranar ta Talata a yankin Dopemu da ke a jihar.
- Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Zama Nagge Dadi Goma
- Xi Ya Shiryawa Manyan Baki Liyafar Girmamawa
An ruwaito cewa, jami’an kiwon lafiya na gaggawa sun yi saurin zuwa wajen da hatsarin ya auku don bayar da agajin gaggawa.
Ba a dai tabbatar abin da ya janyo aukuwar hatsarin ba, amma an ruwaito cewa, mahukunta sun fara gudanar da bincike domin kare sake aukuwar hakan, a gaba.
Irin wadannan motocin hayar na bas na BTR, suna yawan yin hatsari a birnin na jihar Legas.