Da safiyar Lahadin nan ne, jiragen sama dauke da fasinjoji na farko da ba sa bukatar bin tsauraran matakan yaki da annobar COVID-19 suka sauka, a filayen jiragen saman biranen Guangzhou da Shenzhen dake lardin Guangdong na kudancin kasar Sin.Â
Hukumar Kwastam ta kasar ta ce jiragen saman 2, dauke da fasinjoji 387, sun taso ne daga birnin Toronto da kasar Singapore, sun kuma sauka yau Lahadi, ranar da kasar Sin ke kawo karshen aiwatar da tsauraran matakan shige da ficen fasinjoji sakamakon bazuwar cutar COVID-19.
A cewar babban daraktan hukumar Yu Jianhua, matakan kandagarki da yaki da cutar COVID-19 na Sin, sun yi matukar inganta, kuma wajibi ne a aiwatar da su, tare da daidaita ayyukan kwastam sannu a hankali cikin tsari.
A wani ci gaban kuma, a dai yau Lahadin, yankin musamman na Hong Kong, ya bude damar zirga-zirgar fasinjoji tsakanin sa da babban yankin kasar Sin. A lokaci guda kuma, al’umma sun fara tafiye tafiye tsakanin yankunan kan iyakar kasar ta Sin.
A watan Disamban da ya gabata ne kasar Sin ta sanar da dage tsauraran matakan yaki da COVID-19, wadanda suke bukatar matafiya daga kasashen waje dake shigowa kasar yin gwajin kwayoyin cutar COVID-19, tare da bukatar su da su killace kan su tsawon wasu kwanaki.
A yanzu, fasinjoji masu shigowa kasar na bukatar nuna shaidar gwaji ta tsawon sa’o’i 48 ne kawai kafin hawowa jirgi zuwa kasar, kuma ba bu bukatar neman takardar shaidar musamman ta ingancin lafiya, daga ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen waje kafin shigowa kasar. (Saminu Alhassan)