Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, za ta yi tattaunawa da kwararru a duniya kan sauyin da take son kawo wa a harkokin saye da sayerwar ‘yan wasa, bayan hukuncin kotu kan musayar da aka yi wadda aka amince ta karya dokokin Tarayyar Turai.
A farkon wannan watan ne kotun Tarayyar Turai ta yi wani hukunci kan karar tsohon dan wasan Chelsea da Arsenal da kuma tawagar ‘yan wasan kasar Faransa, Lassana Diarra, kan abin da ya ce batanci da FIFA ta ja masa.
- Hadin Gurasa Na Zamani
- Gwamnatin Kebbi Ta Kafa Kwamitin Kwato Kuɗaɗen Da Aka Sace A Asusun Marayun Jihar
Hukuncin ya ce, lokacin da za a dauki dan wasan da wa’adin zamansa a kungiya ya kare ba kuma a sabunta ba, kungiyoyi za su hadu wajen biyan tsohuwar kungiyar dan wasan idan soke kwantaraginsa ta yi ba tare da wata dalili ba.
Diarra ya ce dokar ta dakile masa ‘yancinsa na yawace-yawace bayan soke kwantaraginsa da kungiyar Lokomotib Moscow ta Rasha a shekarar 2014, wanda hakan ya karya dokar gasanni a fadin duniya baki daya.
Kotun ta amince cewa FIFA ta hana Diarra shaidar musayar kungiya ta ITC domin komawa kungiyar Charleroi dake Belgium a shekarar 2015, wanda hakan ya nuna yadda hakan ya dakilewa danwasan ‘yancinsa na tafiye-tafiye da zai ba shi damar samun wata kungiya sabuwa.
FIFA ta ce yanzu za ta bude wani zauren tattaunawa na duniya domin bai wa masu ruwa da tsaki damar fadin albarkacin bakinsu domin amfani da sabuwar dokar wadda za ta kawo sauyi ga rayuwar ‘yan wasa a duniya.