Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Idan ba a manta ba a karatunmu na makon da ya gabata mun tsaya ne a kan ayoyin da Manzon Allah (SAW) ya gani a lokacin da ya yi Mi’iraji. Isara’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW) duka suna nuna mana girman darajarsa ne a wurin Allah Tabaraka wata’ala.
A Mi’iraji, Manzon Allah (SAW) ya ga Rafrafu, ya ga Jibrilu, ya ga Al’arshi, ya ga Kursiyyu, ya ga Magaryar Tikewa, ya ga Mustawad Darafaini (wani irin waje ne da misali idan ka yi kudu sai ka fito yamma, idan ka yi sama sai ka fito kasa, abu ne da ya fi karfin hankali).
To amma me ya sa aka ce Manzon Allah ya ga wani bangare ne daga cikin ayoyin Ubangijinsa? Domin kamar yadda ayar ta ce “lakad ra’a min…”, ita “min” tana nuna wani bangare ne na abu, ma’ana ba duka ba. Amma kuma sai ga shi a wani wuri Allah ya ce ya nuna wa Annabi Ibrahim (AS) mulkinsa na sama da kasa, shi ba a ce wani bangare ba. Shi kuwa Manzon Allah (SAW) sai aka ce an nuna masa wani bangare ne na Sarautar Allah. Kuma sannan duk mai imani ya san ba a hada Manzon Allah (SAW) da kowa a sikelin girma da daraja a duk Halittar Allah.
Yadda abin yake shi ne, Malamai sun ce idan an nuna wa Annabi (AS) mulkin sama da kasa baki daya bai kai ko dan kadan daga Sarautar Zatin Allah ba da aka nuna wa Manzon Allah (SAW). Don haka girman abin da Manzon Allah ya gani ya fi na wanda aka nuna masa mulkin sama da kasa. Domin fitar da abin baro-baro, kamar wani Sarki ne ya yi baki mutum biyu, sai ya sa a je da daya daga cikinsu a nuna masa gidajen gonan da yake da su da abubuwan da ke ciki amma Sarkin bai yarda ya gan shi ba. Na biyun kuma Sarkin ya yarda ya shigo har inda yake sun yi magana da komai, ka ga ai wanda aka yarda ya gana da Sarkin nan ya fi girman daraja da komai.
Masu Tafsiri sun yi sabani cikin fassarar ‘Wannajmi’ da aka ce Allah ya yi rantsuwa da Tauraron Surayya. Malaman suka ce wannan fassarar ta cewa ayar tana nufin Tauraron Surayya ne tana nan. Allah yana da ikon ya yi rantsuwa da komai a cikin halittarsa. Amma kuma ayar tana nufin Allah ya yi rantsuwa da Alkur’anin ne kansa ba ayar kawai ba. Domin Alkur’ani haske ne mai haskakawa, saboda haka shi ne Allah yake nufi da Tauraron a wurin wasu Malamai.
An karba daga Ja’afar bin Muhammad (Sharifi, Jinin Manzon Allah SAW) cewa, Tauraron da ake nufi na ‘Wannajmi’ Manzon Allah ne. A wata ruwayar kuma daga wajensa, ana nufin Zuciyar Annabi Muhammadu ne (SAW). Wato Allah ya yi rantsuwa da Zuciyar Annabi Muhammadu (SAW) wacce ta iya daukar abin da idonsa ya gani. Da yawa mutum zai iya ganin abin tsoro sai zuciyarsa ta buga ya mutu. Farkon abin da yake fara bugawa a jikin Dan Adam idan ya ga wani abin tsoro ko na farin ciki; zuciyarsa kafin sauran dukkan jiki. Amma zuciyar Annabi (SAW) da Allah ya rike ta ta iya daukar Alkur’ani, ta ga wadannan ayoyi na ban-mamaki har ma ta ga Allah da kansa SWT (kamar yadda Abdullahi bin Abbas RA ya fada a Tafsirinsa).
Shehu Ibrahim Inyass (RA) yana cewa Malaman da suka ce Manzon Allah bai ga Allah ba, Mala’ika ya gani har yau dai ana nan. In Manzon Allah zai iya ganin Mala’ika (Jibrilu) da fukafuki dubu dari shida (600,000) kuma ko wane fuffuke daya ya rufe mahudar rana da mafadarta, don ya ga Allah ai babu mamaki. Mu yanzu kamar yadda Shehu ya ce mun san zakara mai fukafuki biyu amma idan aka ce ga wani zakara mai fukafuki uku, a ina na ukun yake? To amma na wannan Mala’ikan fa dubu dari shida. Sannan shi Mala’ikan (Jibrilu AS) ya ce idan ya zo gaban Mika’ilu (AS) kamar an kawo kwai ne a gaban giwa.
‘Yan’uwa Musulmi mu ga girman Annabi (SAW). Idan mutum ya ga Aljani yanzu sai an ma sa rukiyya da magunguna ana cewa ya yi gamo. Shi Aljanin da mutumin nan ya gani shi ma idan ya ga Mala’ika sai an ma sa rukiyya don shi ma ya yi gamo. Amma sai gashi Allah ya buda wa Manzon Allah (SAW) yana ganin wadannan abubuwa na ban-mamaki, ai ko daga nan ka san bambancinsa da sauran mutane yana da yawa (SAW). Don haka Ja’afar bin Muhammad (RA) ya ce Allah ya yi rantsuwa da zuciyar Annabi Muhammadu (SAW) a fassarar ‘Wannajmi’.
Haka nan da Allah ya yi rantsuwa da sama da tauraron da ke fitowa da dare mai haske (wassama’i waddarik). Wasu daga cikin Malamai sun ce hakika wannan tauraron ana nufin Annabi Muhammadu (SAW). Idan an tafi a kan wannan fassara, ma’anar ita ce Allah yana rantsuwa da sama tun ba kowa ba komai ya bayyanar da hasken Manzon Allah. Malam Sulamiy ya fadi wannan karatun. Wadannan ayoyi sun tattare abubuwa da yawa na daga girmanan Manzon Allah (SAW) da daukakarsa mai yawa wanda ba za a iya kirgawa ba.
Allah Tabaraka wata’ala ya yi rantsuwa a bisa shiriyar Manzon Allah (SAW) da tsarkinsa a kan cewa ba zai nuna son zuciya ba. Wato ana nufin inda Allah ya ce ‘Maadalla saahibukum wa maa gawa’. Kuma Allah ya yi rantsuwa a kan gaskiyarsa (SAW) cikin duk sakon da ya isar ga halitta baki daya. Allah yana cewa “wamaa yandiku anil hawa…. Yuhaa”, Manzon Allah bai fadar son zuciya face abin da Allah ya yi ma sa wahayi.
Malaman Luga suka ce yana daga abin mamakin Alkur’ani, Allah bai ce ‘wama yata kallamu anil hawa ba’, wato magana a bisa son rai, sai ya ce “yandiku” wadda ke nufin “furuci”. Ko “taf” mutum ya ce da bakinsa; ya yi furuci. To ko haka idan aka ji Manzon Allah ya fada ba son rai ba ne, Allah ne ya yi mai wahayin ya fada kamar yadda Mala’ika Jibrilu (AS) ya isar gare shi. Cewa Mala’ika ne ya isar gare shi wata hikima ce daga Allah don a nuna mana darajar koyo. Annabi (SAW) ya fi Jibrilu kusanci da Allah amma kuma shi ne aka aiko don a nuna wa Dan Adam koyo. Ba ma karatu ba kawai, hatta sana’ar da mutum ya je ya koya a wurin wani ta fi sana’ar da ya koyar da kansa da kansa. Kuma duk abin da ka koya da ladabi a wurin wani sai ka ga albarkarsa. Bare kuma wannan Alkur’ani, lallai mutum zai iya dauka ya karanta amma akwai wasu wurare da suke da wuya wanda dole sai malamin Alkur’anin ne zai iya bayani.
Allah ya ba da labari a kan fifikon Manzon Allah (SAW) a cikin kissar Isra’i. Allah ya bayyana tafiyar Manzon Allah har zuwa Sidratul Muntaha (Magaryar Tikewa), kuma ya ce Manzon Allah ya gaskata abin da idanunsa ya gani. Manzon Allah (SAW) ya ga wasu ayoyin Ubangijinsa masu girma. Allah ya fadakar da mu bisa irin girman darajar Manzon Allah (SAW) a wurinsa da kissar farkon ayar Suratul Isra’i.
Tafiyar da Manzon Allah (SAW) ya yi daga Makkah zuwa Baitil Makdis (Isra’ila a yanzu) daga bayan Isha’i kuma ya je ya dawo mutane ba su tashi daga barci ba, ai wannan ya isa abin mamaki. To amma kuma ba wannan ne abin mamakin ba; idan aka ce daga can Baitul Makdis ya hau sama har zuwa inda Allah ya fada ‘Sidratul Muntaha’ kuma ya dawo, ai duk ya fi ban mamaki. Shi ya sa Allah ya bude farkon ayar Suratul Isra’i da nuna girmansa (SWT) tukuna da ya ce “Subhana” wato “tsarki ya tabbata ga Ubangiji”. Wannan ya sa Dan Adam Musulmi idan wani abu ya ba shi mamaki sai a ji yana fadar “Subhanallah”.
Allah (SWT) ya ce “Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya yi tafiya da bawansa (Annabi Muhammadu SAW) cikin dare daga Masallacin Allah mai alfarma (Ka’aba) zuwa Masallacin nan mai nesa (Baitil Makdis), Masallacin nan da muka yi albarka daura-da-shi (duk kasashen wuraren nan masu ni’ima ne, shi ya sa Turawa yau suka dage sai Isra’ila ta mallaki wurin don sun san meye Allah ya fada a kan wurin) don mu nuna ma sa ayar kanmu, shi (Manzon Allah) mai ji ne; mai gani ne”. Kamar yadda Allah ya ba Manzon Allah (SAW) sunayensa na “Ra’ufu” da “Rahimu”, haka nan ma a wannan ayar ya ba shi “Sami’u” da “Basiru”. Sauran ‘Yan Adam ma sun samu wannan saboda albarkar Manzon Allah (SAW). A cikin suratul Insan (Sura ta 76, aya ta 2), Allah ya tabbatar da haka, a inda ya ce “mun san ya shi (Dan Adma) mai ji; mai gani”
Tun daga lokacin da wannan ayar ta Suratul Isra’i ta sauka har zuwa yau tana nuna Mu’ujizar Manzon Allah (SAW). Allah Ta’ala yana nuna mu al’ummar Annabi za mu rika hawa sama, ga shi nan muna ta yi ta jirgi. Yanzu idan mutum ya tashi daga Kaduna zai je Makkah bayan isha’i, zai iya sauka a can har ya tafi wani wuri abin sa gari bai waye ba. Haka nan daga Makkah din zuwa Isra’ila, duk mutum zai iya zuwa cikin daren. A tafiyar ta Isra’i, Manzon Allah (SAW) tuka shi aka yi a kan buraka. Al’ummarsa ta yanzu mu ma mun samu irin wannan girma, domin mutum zai zauna a abin hawa ana tuka shi wani sa’in ma har da yin barci. Mutum barci yake yi amma kuma tafiya ake, duk saboda Mu’ujizar Manzon Allah (SAW).
Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu ji tsarkakewar da Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) a tafiyar da ya yi na Isra’i da Mi’iraji.
Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.