Wani fim da aka nuna domin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya, ya yi matukar jan hankulan masu kallo a Nijeriya, lamarin da ya haifar da waiwaye game da muguntar da aka tafka a yakin da kuma darussan da za a koya a wannan zamanin. Kallon fim din wanda ofishin jakadancin kasar Sin da ke Nijeriya ya shirya a ranar Jumma’ar da ta gabata, ya samu halartar dimbin ‘yan Nijeriya da Sinawa mazauna kasar.
Wani mai sharhi kan al’amuran duniya Lawal Sale, ya bayyana cin zalin da Japanawa suka yi wa al’ummar kasar Sin a matsayin “mummunan laifi ga bil’adama,” inda ya kara da cewa, jajircewar da Sinawa suka nuna wajen yin kasada da rayukansu don kiyaye hotunan shaidun irin ta’asar da sojojin kasar Japan suka tafka, sun yi matukar burge shi.
Da yake jawabi gabanin nuna fim din, jakadan kasar Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, yana mai jaddada wajibcin kiyaye zaman lafiya, da adalci, da ka’idojin kafuwar MDD.
Yu ya ce, kasar Sin ta tafka asarar rayukan sojoji da fararen hula sama da miliyan 35 da kuma asarar tattalin arzikin da ya zarce dalar Amurka biliyan 600 a lokacin yakin duniya na biyu. Ya yi nuni da cewa, tsayin dakan da kasar Sin ta yi ya yi mummunar wargaza mulkin danniya, tare da ba da gudummawa mai tarihi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp