Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal.
Wanda aka yi amfani da ingantattun shaidun hotuna na ta’asar yakin da Japanawa suka aikata a lokacin kisan kiyashin Nanjing, Fim din na “Dead to Rights” ya ba da labari ne na wani rukunin fararen hula na kasar Sin da suka nemi mafaka a dakin daukar hoto a lokacin muguwar mamayar da azzaluman Japanawa suka yi a birnin Nanjing.
A wani yunkuri na neman tsira da rayukansu hajaran-majaran, an tilasta musu taimaka wa wani mai daukar hoto na sojan Japan wajen wanke hotuna, amma kwatsam suka gano dodon hotunan yana dauke da shaidun munanan ta’asar da sojojin Japan suka tafka a sassan birnin. Bisa kudirinsu na tona asirin abin da ya faru, sai suka boye dodon hotunan tare da jefa rayuwarsu cikin hadari wajen bayyana su ga duniya.
Bisa kididdigar da aka yi na baya-bayan nan, ana sa ran “Dead to Rights” zai samu kudin shiga fiye da yuan biliyan 4, inda aka samu karin kiyasin da aka yi a baya. Idan har aka cimma burin hakan, zai zama fim na biyu mafi samun tagomashi a kasar Sin a bana, inda ya biyo bayan fim din “cartoon” na “Ne Zha 2.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp