Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa, NFF ta nada tsohon ɗan wasa, Finidi George a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya.
Sanarwar da hukumar ta fitar da yammacin ranar Litinin, ta bayyana cewa, nadin yazo ne sakamakon nazari da kwamitin nada mai koyarwa na hukumar ya yi a kansa.
- Watanni 3 Da Naɗa Shi Shugaban Hukumar NCAA, Capt. Najomo Ya Sayi Motar Miliyan 250
- Wani Shahararren Dan Boko Haram Ya Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
Finidi George, mai shekaru 52 a duniya, shi ne mataimakin kocin tawagar Super Eagles, Jose Poseiro, wanda ya ajiye aiki bayan kammala wasannin kofin Afirka da Nijeriya ta kai wasan karshe.
Tsohon ɗan wasan na Ajax da Real Betis ya shafe watanni 20 a matsayin mataimakin kocin na Super Eagles kuma shi ne ya ja ragamar Nijeriya a wasan sada zumunta da Super Eagles ta yi da Ghana, wasan da Nijeriya ta samu nasara da ci 2-1.
Yana ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarar 1994 da aka buga a Tunisia sannan ya wakilci Super Eagles a gasar cin kofin duniya da aka buga a Amurka a shekarar 1994 da wanda Faransa ta karɓi bakunci a shekarar 1998.
Babban aikin da ke gabansa a yanzu shi ne, jagorantar Nijeriya wajen samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 da ƙasashen Amurka da Mexico da Canada za su karɓi bakunci.