Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya gabatar da kiyasin Naira 225,893,690,626 a gaban majalisar dokokin jihar a matsayin kasafin kudin shekarar 2024.
Haka kuma gwamnan ya yi godiya game da goyon bayan da majalisar dokokin jihar ke bai wa gwamnatimsa.
- Shugabancin JKS Ya Gudanar Da Taro Game Da Ayyukan Raya Tattalin Arzikin Kasa Na 2024
- Kyautata Rayuwar Matasa Ne Fatanmu – Kwamoti La’oriÂ
Ya nemi karin goyon baya domin hadin kai da ayyukan ci gaba da jama’ar jihar.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya shaida wa ‘yan majalisar irin tanadin da ke kunshe cikin kasafin kudin, domin kyautata walwala, yanayin rayuwa da ma kyautata jin dadin jama’a a shekarar 2024, mai zuwa.
Ita ma dai tun a ranar Larabar da ta gabatar, majalisar zartaswar gwamnatin jihar ta amince ta kiyasin kasafin kudin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp