An kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa na kasa wato CIIE karo na 8 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar a ranar 5 ga watan Nuwamba, inda kasar Georgia ke halartar bikin cikin shekaru 8 a jere, kuma a bana tana cikin kasashen da suka samu matsayin Manyan Baki (Guests of Honor) a wurin bikin.
Wakiliyar babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ta samu damar zantawa da firaministan kasar Georgia, Irakli Kobakhidze wanda ya halarci bikin a Shanghai, inda ya bayyana cewa, baje kolin CIIE wani dandali ne mai matukar muhimmanci, wanda zai bayar da babbar gudummawa ga karfafa huldodin Sin da Georgia ta fuskokin tattalin arziki da kasuwanci, yana kuma mai fatan kasarsa za ta kara amfani da damarmakin hadin-gwiwa da kasar Sin a nan gaba.
A matsayin irinsa na farko a duk fadin duniya da ke maida hankali kan batun shigowa da hajoji, CIIE ta dade da cika alkawarin “kara kyautata ayyukan CIIE” tun kafuwarsa a shekara ta 2018, bikin da ba kafa wani budadden dandali na musanyar nasarori tsakanin kasa da kasa kawai ya yi ba, har ma ya sanya kuzarin kasar Sin ga habakar tattalin arzikin duniya bisa nasarorin tattalin arziki da kasuwanci na zahiri da aka samu a wajen bikin. (Murtala Zhang)














