Yayin da yake zantawa da ’yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa, Xi Jinping shugaban kasa ne mai matukar hangen nesa.
A cewar firaministan, Xi Jinping, shugaban kasa ne wanda ke mayar da hankali sosai kan kyautata rayuwar jama’a, kuma a karkashin jagorancinsa, kasar Sin ta samu nasarar yaki da matsanancin talauci, al’amarin da ke bukatar matukar hangen nesa da babbar hikima. Kazalika, shugaba Xi yana amincewa da ra’ayin cudanyar sassan kasa da kasa.
Firaminista Shehbaz ya kara da cewa, ba sauya yanayin tattalin arzikin kasar Sin kawai shugaba Xi ya yi ba, har ma ya mayar da kasar zuwa matsayi na biyu a karfin tattalin arziki a duniya, kuma babbar kasa mai karfin soja. Ya ce abu mafi muhimmanci a nan shi ne, shugaba Xi ya dade yana dukufa kan taimaka wa sauran kasashe ta yadda za su mori nasarorin da kasar Sin ta samu, tare da kokarin inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe, ta yadda kasashe masu karamin karfi su ma za su iya cin gajiya, kuma jama’arsu za su iya ficewa daga kangin talauci, da jin dadin nasarorin da aka samu wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp