A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi.
A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori wajen inganta hadin-gwiwar kasashensu a fannoni daban-daban. A yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka yi a watan Satumban bara a Beijing, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan daga matsayin huldar kasashensu, zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, al’amarin da ya kafa alkibla ga ci gaban dangantakarsu.
Firaminista Li ya ce yana fatan kara kokari tare da Nestor Ntahontuye, don aiwatar da muhimman ra’ayoyi iri daya da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, gami da nasarorin da aka samu a wajen taron kolin FOCAC na Beijing, ta yadda nasarorin dangantakar Sin da Burundi za su kara amfana wa al’ummominsu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp