Da safiyar yau Asabar 9 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci zama a mataki na farko na taron koli karo na 18, na shugabannin kasashen G20 wanda a yanzu haka yake gudana a birnin New Delhin kasar Indiya, inda ya kuma gabatar da jawabin dake cewa, ya dace kasashe membobin kungiyar G20 su tsaya kan zama tsintsiya madaurinki daya, da daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya da samar da ci gaba.
Li ya ce, dan Adam na da makoma ta bai daya, kana, ya kamata kasashen duniya su mutunta juna, da neman kamanceceniya duk da cewa akwai bambancin ra’ayi, da kuma zaman jituwa tare.
Firaministan ya kuma jaddada cewa, kasarsa za ta tsaya kan zurfafa yin gyare-gyare a gida, da fadada bude kofa ga kasashen waje, da samar da ci gaba mai inganci, da zamanantar da kasar Sin bisa salonta. Kasar Sin na da makoma mai haske, wadda babu shakka za ta kara sanya kuzari ga farfado da tattalin arzikin duniya da samar da ci gaba mai dorewa.
Kasar Sin za ta hada gwiwa tare da sauran kasashe, domin kara azama da bayar da karin gudummawa ga duk duniya da makomar dan Adam baki daya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp