A jiya jumma’a ne firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar gibin kudi na samun bunkasuwa a duniya, kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su hada kai da gaske, da yin aiki tare don warware matsalolin da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashe masu rauni suke fuskanta.
A jawabin da ya gabatar a wajen bikin rufe taron koli na sabuwar yarjejeniya ta samar da kudade ta duniya, Li ya gabatar da shawarwari mai kunshe da abubuwa uku dangane da hakan.
Na farko, ci gaba da yin garambawul ga tsarin tafiyar da harkokin hada-hadar kudi na duniya da samar da ingantaccen yanayin samar da kudade ga kasashe masu tasowa.
Na biyu, gina haɗin gwiwar ci gaban duniya da samar da ƙarin albarkatun ci gaba ga ƙasashe masu tasowa. Kasashen da suka ci gaba ya kamata su mutunta alkawurran da suka dauka na ba da taimako da kudade ga kasashe masu tasowa. Ya kamata kasashe masu tasowa su kara inganta karfinsu na raya kansu.
Na uku, inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya da cinikayya cikin ‘yanci don sanya sabbin ci gaba a kasashe masu tasowa.
Li ya jaddada cewa, a duniyan nan da ke cike da cece-kuce da rashin tabbas, kamata ya yi kasashen Sin da Turai su nemi matsaya guda tare da kiyaye bambance-bambance, da fadada hadin gwiwa tare da takaita bambancin ra’ayi, da inganta hadin gwiwar kirkire-kirkire, da tinkarar rashin tabbas na yanayin kasa da kasa tare da daidaita dangantakar Sin da Turai, da kuma haɓaka ci gaban ɗan adam mai dorewa tare. (Yahaya)