Firaministan kasar Malaysia Anwar Ibrahim ya zanta da wakiliyar CMG yayin da ya kawo ziyara kasar Sin kwanan baya, inda ya yaba da shawarar wayewar kan kasa da kasa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
Firayin minista Anwar ya yi tsokaci cewa, tunanin da shawarar ta nuna yana shafar daukacin bil Adam, saboda gudanar da shawarwari kan wayewar kai bisa tushen martaba juna yana da muhimmanci matuka, don haka kasashen duniya suna iya tinkarar matsalolin da za su fuskanta a nan gaba bisa ruhin shawarar. An lura cewa, yanzu wasu shugabannin gwamnatocin kasashen duniya, sun fi mai da hankali kan hakikanin abubuwa dake gabansu, amma shugaba Xi ya bayyana tunaninsa kan daraja da al’ada da kuma wayewar kai, duk wadannan sun dace da muradun al’ummar Malaysia, wadda kasa ce mai kalibu da addinai daban-daban, yana ganin cewa, muddin aka martaba saura, tare da fahimtar wayewar kai da al’adu da sakamakon da suka samu, babu shakka za su cimma matsaya daya. (Mai fassarawa: Jamila)