Firaministan Nepal Khadga Prasad Sharma Oli, ya ce Sin ta samu cikakken ci gaba, kuma daga dukkanin fannoni, wanda ya hada da raya ilimi, da kiwon lafiya, da bunkasa tattalin arziki, da samar da manyan ababen more rayuwa, da bunkasa kimiyya da fasaha na zamani. Sauran sun hada da zamanantar da zamantakewar al’umma baki daya, da aikin noma, da raya masana’antu, da cinikkaya da kasuwanci, da kuma kare muhalli da sauransu.
Mista Oli, ya bayyana hakan ne kwanan baya, yayin zantawarsa da ‘yar jarida ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG. Game da gudummawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar a fannin inganta bunkasuwar Sin kuwa, Oli ya ce shugaba Xi Jinping ya sa kaimi ga bunkasa dukkan fannonin rayuwar zamantakewar kasarsa, ciki har da ci gaban tattalin arziki, da mulkin kasa, da kuma gudanar da ayyukan jam’iyya. Ya ce Xi shugaba ne mai hangen nesa, kuma muradun da ya gabatar kafin shekaru goma sun zama gaskiya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp