Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi.
Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi. Abin da ya yi matukar ba shi mamaki shi ne yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye labarun abubuwan da suka faru da su. Wannan girmamawa da ci gaba da raya tarihi su ne ainihin ginshikin tabbatar da cewa ana gadar wa zuriyoyi da wannan haske.
Sonko ya ce, al’ummar kasar Sin sun tuna da tarihinsu, wanda hakan ya sa ya zama sinadarin hadin kan kabilu, kuma wani muhimmin karfi da ke kara zaburar da jama’ar kasar Sin su kai ga kokarin bunkasa kasarsu, kana ya ce, hakika wannan yana da matukar muhimmanci. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp